Matasa ga na ku: Yul Edochie ya fito takarar Shygaban kasar Najeriya

Matasa ga na ku: Yul Edochie ya fito takarar Shygaban kasar Najeriya

- Edochie ya fito takarar Shugaban kasar nan a zabe mai zuwa

- ‘Dan wasan yace ya dai zama dole a samu shugabanci na-gari

- Edochie zai yi takara ne da Shugaba Buhari a karkashin APGA

Mun kawo maku labari cewa ‘Dan wasan fim din na Najeriya Yul Edochie ya fara harin Shugaban kasa inda yace a zaben 2019 zai doke Shugaba Muhammadu Buhari daga kujerar sa.

Yul Edochie zai tsaya takarar Shugaban kasa a 2019

Yul Edochie yayi takarar Gwamnan Jihar Anambra kwanan nan amma bai kai labari ba. Edochie ya fara takarar ne a karkashin Jam’iyyar DPC kafin ya sauya sheka zuwa Jam’iyyar APGA daga baya ‘yan watanni kadan da su ka wuce.

KU KARANTA: Orji Uzor Kalu ya nemi a zabi Buhari a 2019

Fittacen ‘Dan wasan kasar Yul Edochie yace Najeriya na da tarin albarka amma tana fama da matsalar shugabanci. Edochie ya bayyana wannan ne a shafin sa na sadarwa na zamani na Tuwita ba da jimawa ba kamar yadda mu ka ji.

Edochie yace wannan mulki na shirme da ake fama da shi a kasar ya isa haka domin kuwa kura ta kai bango ya fito takara a APGA domin kawo karshen matsalar. A baya dama dai ‘Dan wasan ya Shugaba Buhari shawara ya hakura da 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel