Ina fatan kada Allah yasa Najeriya ta sake fuskantar yakin basasa - Gowon

Ina fatan kada Allah yasa Najeriya ta sake fuskantar yakin basasa - Gowon

Tsohon shugaban kasa, Janar Yakubu Gowon ya nuna dacin rai akan tarin matsalolin da kasar ke fuskanta a kwanakin nan musamman na tsaro da yawan kashe-kashen da akeyi a kasar.

Ya bayyana hakan a matsayin abun damuwa.

Gowon wanda ya halarci taron addu’o’i na musamman a Yenagoa ya bayyana cewa yayi addu’a tare da fatan cewa kasar bazata sake fuskaantar matsala ba a karshen yakin basasar Najeriya.

Yace baya fatan kasar ta sake shiga kunci da kunar rai irin na baya ba.

Ina fatan Allah kada yasa Najeriya ta sake fuskantar yakin basasa - Gowon

Ina fatan Allah kada yasa Najeriya ta sake fuskantar yakin basasa - Gowon

Ya zanta da manema labarai jim kadan bayan wani addu’a na musamman a cocin Yenagoa a ranar Lahadi.

KU KARANTA KUMA: Saraki da Tambuwal sun bawa PDP ka’idoji na dawowa jam’iyyar

Yayi Allah wadai da hare-haren ta’addanci wanda makiyaya da Boko Haram ke kaiwa.

Ya bayyana cewa shugabannin kasar basa iya bacci saboda wannan lamari.

Sannan kuma ya bukaci jama’a da su ba gwamnati goyon baya wajen ganin an magance matsalolin tsaro.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel