Yanzu-yanzu: An saki Sanata Dino Melaye

Yanzu-yanzu: An saki Sanata Dino Melaye

Sanata mai wakiltan mazabar Kogi ta yamma, Dino Melaye, ya fita daga hannun hukumar shiga da fice.

An saki sanatan ne ayan jami’an hukumar shiga da fice wato Immigration suna damke shi a babban filin jirgin saman Nnamdi Azikwe da ke Abuja yayinda yayi niyyar tafiya kasar Maroko.

Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa Hukumar shiga da ficen Najeriya ta tabbatar da damke Sanata Dino Melaye a babban filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja da safen nan.

Kakakin hukumar, Mr Sunday James, ya bayyanawa manema labarai cewa sun kama Dino Melaye ne bisa ga umurni da aka basu.

Sun tabbatar da wannan labari ne bayan Sanatan ya bayyana a shafinsa na Tuwita cewa an kama shi yayinda yake kokarin fita kasar waje.

Legit.ng ta kawo muku cewa Sanatan ya wallafa a shafinsa na Twitter a safiyar ranar Litinin, 23 ga watan Afrilu, sanatan yace an kama shi ne a hanyarsa ta zuwa Morocco domin ziyarar aiki.

Melaye ya rubuta: “Yanzun nan aka kama ni a filin jirgin sama na Abuja wato Nnamdi Azikiwe airport a hanyata na zuwa Morocco domin gudanar da wani aiki da yardar gwamnatin tarayya.”

KU KARANTA: Dalilin da ya sa muka kama Dino Melaye – Hukumar shiga da fice

Za ku tuna cewa hukumar yan sandan Najeriya ta alanta neman Dino Melaye ruwa a jallo bisa ga zargin daukian nauyin wasu yan baranda a jihar Kogi. Read more: https://hausa.legit.ng/1165157-dalilin-da-ya-sa-muka-kama-dino-melaye-hukumar-shiga-da-fice.html#1165157

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel