Saraki da Tambuwal sun bawa PDP ka’idoji na dawowa jam’iyyar

Saraki da Tambuwal sun bawa PDP ka’idoji na dawowa jam’iyyar

- Bukola Saraki da Tambuwal da wasu tsofaffin ‘yan jam’iyyar sun bawa jam’iyyar ta PDP ka’idar canja suna kafin su amince su koma jam’iyyar

- Jam’iyyar ta PDP tanata ta maganganu akan Saraki, Gwamna Tambuwal da Sanata Aliyu Wammako, tsohon gwamnan jihar Kano Rabi’u Kwankwaso da tsohon gwamnan jihar Gombe Danjuma Goje game da bukatar su dawo jam’iiyar don karbar mulki daga hannun jam’iyyar APC

- Jigon na jam’iyyar APC wadanda akewa kirari da “game changers” sun samu rashin aminta daga masu zartarwa na jam’iyyar ta PDP

Bukola Saraki da Tambuwal da wasu tsofaffin ‘yan jam’iyyar sun bawa jam’iyyar ta PDP ka’idar canja suna kafin su amince su koma jam’iyyar gabannin zaben shekara mai zuwa.

Jam’iyyar ta PDP tanata ta maganganu akan Saraki, Gwamna Tambuwal da Sanata Aliyu Wammako, tsohon gwamnan jihar Kano Rabi’u Kwankwaso da tsohon gwamnan jihar Gombe Danjuma Goje game da bukatar su dawo jam’iiyar don karbar mulki daga hannun jam’iyyar APC.

Jigon na jam’iyyar APC wadanda akewa kirari da “game changers” sun samu rashin aminta daga masu zartarwa na jam’iyyar ta PDP, mai gana da yawun jam’iyyar ta PDP Kola Ologbondiyan yayi ikirarin cewa har yanzu jam’iyyar bata yanke wani hukunci ba akan lamarin.

Saraki da Tambuwal sun bawa PDP ka’idoji na dawowa jam’iyyar

Saraki da Tambuwal sun bawa PDP ka’idoji na dawowa jam’iyyar

Akwai yiwuwar idan aka canjawa jam’iyyar suna aka mayar da ita “game Changer” zata kawo karshen kwamitin jagorancin tarayya (NWC) na jam’iyyar, wanda Prince Uche Secondus ke shugabanta.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: An kama Sanata Melaye a filin jirgin sama

Wasu daga cikin jagororin jam’iyyar ta PDP suna nuna cewa bai kamata wasu da suka gudu daga jam’iyyar ba lokacin da sukaga zata rasa zabe ba, su ringa kawo masu ka’idojin da za’a bi don anaso su dawo jam’iyar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel