Dalilin da ya sa muka kama Dino Melaye – Hukumar shiga da fice

Dalilin da ya sa muka kama Dino Melaye – Hukumar shiga da fice

Hukumar shiga da ficen Najeriya ta tabbatar da damke Sanata Dino Melaye a babban filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja da safen nan.

Kakakin hukumar, Mr Sunday James, ya bayyanawa manema labarai cewa sun kama Dino Melaye ne bisa ga umurni da aka basu.

Sun tabbatar da wannan labara ne bayan Sanatan ya bayyana a shafinsa na Tuwita cewa an kama shi yayinda yake kokarin fita kasar waje.

Dalilin da ya sa muka kama Dino Melaye – Hukumar shiga da fice

Dalilin da ya sa muka kama Dino Melaye – Hukumar shiga da fice

Legit.ng ta kawo muku cewa Sanatan ya wallafa a shafinsa na Twitter a safiyar ranar Litinin, 23 ga watan Afrilu, sanatan yace an kama shi ne a hanyarsa ta zuwa Morocco domin ziyarar aiki .

Melaye ya rubuta: “Yanzun nan aka kama ni a filin jirgin sama na Abuja wato Nnamdi Azikiwe airport a hanyata na zuwa Morocco domin gudanar da wani aiki da yardar gwamnatin tarayya.”

KU KARANTA: An kama Sanata Melaye a filin jirgin sama

Za ku tuna cewa hukumar yan sandan Najeriya ta alanta neman Dino Melaye ruwa a jallo bisa ga zargin daukian nauyin wasu yan baranda a jihar Kogi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel