Sun kwace fasfot dina, nima na fisge abina – Melaye yayi magana akan kamun sa

Sun kwace fasfot dina, nima na fisge abina – Melaye yayi magana akan kamun sa

Dan majalisa mai wakiltan yankin Kogi West, Sanata Dino Melaye yaq bayar da Karin haske akan kamun sad a akayi a filin jirgin Nnamdi Azikiwe.

Yace: “Ni da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu da sauran mutane muna a hanyarmu ta zuwa ziyarar aiki kasar Morocco amma wasunmu zasu bi ta Lagas a gobe.

“Na je filin jirgin nan sannan an duba ni ina jiran tafiya. Jami’an immigration suka gayyace ni wai akwai umurni daga hukumar yan sanda cewa b azan iya tafiya ba; cewa ina cikin wadanda sike nema. Sai nace ba gaskiya bane, cewa INTERPOL basu sanar dani ba. Na bude shafin INTERPOL na nuna masu. Amma sai suka ce lallai umurnin yan sanda ne.

“Sun dawo dani sannan suka bukaci naje ofishinsu na filin jirgin. Suka kwace fasfot dina amma na kwace abina. Ina tare da su har yanzu. Sun zagaye ni sannan suka ce suna jiran umurni daga yan sanda."

Sun kwace fasfot dina, nima na fisge abina – Melaye yayi magana akan kamun sa

Sun kwace fasfot dina, nima na fisge abina – Melaye yayi magana akan kamun sa

A baya Legit.ng ta rahoto cewa an kama Sanata Dino Melaye mai wakiltan Kogi West a filin jirgin sama na Abuja.

KU KARANTA KUMA: Mutane da dama sun jikkata yayinda Yarbawa da Hausawa suka kara a Ondo

A cewar wani rubutu da Sanatan ya wallafa a shafinsa na Twitter a safiyar ranar Litinin, 23 ga watan Afrilu, sanatan yace an kama shi ne a hanyarsa ta zuwa Morocco domin ziyarar aiki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel