Wata sabuwa: Ƴan Boko Haram sunfi jami'an tsaron Najeriya wayo - CAN

Wata sabuwa: Ƴan Boko Haram sunfi jami'an tsaron Najeriya wayo - CAN

- Bayan yiwa shugaban kasa Buhari kashedi, CAN ta sake tutsu ga jami'an tsaro

- CAN dai ta bukaci kowanne Kirista yayi kokarin kare kansa

- Shugaban kungiyar CAN din ne ya fadi haka a yayi wani taronsu

Shugaba ƙungiyar Kiristoci ta ƙasa (CAN) Rev. Ayokunle Olasupo, ya bayyana damuwarsa kan yadda ƴan ta'addan makiyaya da Boko Haram da sauran ƙungiyoyin yan tada kayar baya ke cigaba da ɓullo da dabarun da jami'an tsaron Najeriya suka kasa maganinsu.

Wata sabuwa:Ƴan Boko Haram sunfi jami'an tsaron Najeriya wayo- CAN

Rev. Ayokunle Olasupo

Don haka yayi kira ga mabiya addinin Kirista a duk inda suke da su kare rayuwarsu domin tsira

Olasupo, wanda kuma shine shugaban ƙungiyar Kiristoci mabiya ɗariƙar Baptis (NBC), sannan yayi kira ga mabiya ɗariƙar tasa ta Baptis, da su shiga a dama da su a harkokin siyasa domin kada a barsu a baya.

A cewarsa, Najeriya zata gyaru ne kaɗai idan har Kiristawa ne ke riƙe da madafun iko.

KU KARANTA: Rundunar soji sunyi nasarar kama ‘yan kungiyar asiri 23, Sojan gona da kuma masu fasa bututun man fetur (hotuna)

Malamin cocin ya faɗi hakan ne a cikin ƙarshen makon da mu kai ban kwana da shi a jihar Rivers yayin wani taron addini na shekara-shekara da aka gudanar a garin Ndele, na ƙaramar hukumar Emohua ta jihar ta Rivers.

Da yake magana akan batun kare kan, yace "Lauyoyi sun bayyana cewa kare kan bai saɓa da kundin tsarin mulki ba, kuma abu ne ma da ya dace don tsiratar da rayuwarka".

"Kimanin kusan shekaru tara kenan amma mutane nawa aka kama ko aka hukunta? Duk wanda ya bari haka kawai wasu yan ta'adda suka kashe shi, tabbas ya cika wawa". A cewar Rev. Ayokunle.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel