Rundunar Operation Lafiya Dole sun gano wani sansani na ‘Yan ta’adda

Rundunar Operation Lafiya Dole sun gano wani sansani na ‘Yan ta’adda

- Sojojin Najeriya sun bankado wani wuri da Boko Haram ke shirin fada

- Tuni aka kona wannan filin horon da ke Garin Benisheikh a cikin Borno

- A harin Sojojin Najeriya sun aika wani ‘Dan ta’ddan Boko Haram lahira

Mun samu labari dazu nan daga wani babban Darektan yada labarai na Rundunar Sojojin Najeriya cewa sun hallaka wani ‘Dan Boko Haram guda bayan da su ka gano wani wuri da ‘Yan ta’addan su ke horas da mayakan su a Jihar Borno.

Rundunar Operation Lafiya Dole sun gano wani sansani na ‘Yan ta’adda

Sojojin Operation Lafiya Dole a bakin aiki a Benisheikh

Sojojin Najeriya sun aika wani ‘Dan ta’ddan Boko Haram lahira a lokacin da su ka dura wannan wuri da ke cikin Garin Afa a Ranar Lahadi da sassafe. Tuni dai aka kona wannan filin horon da ke Garin Benisheikh a cikin Borno.

KU KARANTA: Iyalan Boko Haram sun fada hannun Rundunar Sojin Najeriya

Sojojin kasar su na zagayen da su ka saba ne na ganin karshen ‘Yan Boko Haram a Yankin. Sojojin sun yi nasarar harbe wani ‘Dan ta’adda guda har lahira bayan da sauran su ka tsere. An kuma ceto wani da Boko Haram din su ka kama.

Sojojin sun kuma yi nasarar karbe wata bindiga daga hannun ‘Yan ta’addan bayan wannan mutumi mai suna Malam Abba da aka ceto. Onyema Nwacukwu na Sojin kasar ya bayyana wannan a madadin Rundunar Operation Lafiya Dole.

Ku na da labari cewa utane 7 ne suka mutu yayinda 12 suka jikkata a harin da aka kai masallacin Bama a karshen makon nan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel