A bar kaza cikin gashin ta: Yadda na ceci Fayose bayan an tsige shi daga Gwamna – Kalu

A bar kaza cikin gashin ta: Yadda na ceci Fayose bayan an tsige shi daga Gwamna – Kalu

- Tsohon Gwamnan Kasar Inyamurai ya nemi a marawa Buhari baya

- Orji Uzor Kalu yace tattalin Najeriya zai kara habaka ma bayan 2019

- Babban ‘Dan APC ya bayyana yadda su ka yi da Gwamna Fayose a da

Mun samu labari cewa Orji Uzor Kalu yayi kira ga Jama’a su dafawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zarce a 2019 domin ya habaka tattalin arzikin Najeriya idan ya dawo. Uzor Kalu yace Gwamnatin Jonathan tayi mugun barna.

A bar kaza cikin gashin ta: Yadda na ceci Fayose bayan an tsige shi daga Gwamna – Kalu

Uzor Kalu yace Jonathan ya tabarbara kasar nan

Jigon na Jam’iyyar APC yace idan Buhari ya zarce zai maida hankali ne kan tattali. Tsohon Gwamnan na Abia wanda rikakken ‘dan kasuwa ne mai Ma’aikata kusan 10, 000 yace sam ba za su bari Shugaba Buhari ya gaza ba idan ya dawo mulki.

KU KARANTA: An tarwatsa taron da magoya bayan Buhari su ka shirya a Jigawa

Uzor Kalu a wata hira da Jaridar Jaridar Punch yace Gwamnatin Jonathan ta kashe kasar nan saboda irin satar da aka rika tafkawa a lokacin sa maimakon ayi wa kasa aiki. Kalu yace Shugaba Buhari ya karbi kasar ne a lalace kuma yana bakin kokari.

Tsohon Gwamnan ya kuma bada labari cewa shi ne ya ceci rayuwar Gwamnan Ekiti Ayo Fayose a 2003 bayan an tsige shi daga kujerar Gwamna ya kawo shi cikin gidan sa a Legas. Kalu yace shi ya rika ba sa abinci saboda kar a sa masa guba a lokacin

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel