An kama wani mutumi bisa zargin yiwa yar shekara 13 fyade

An kama wani mutumi bisa zargin yiwa yar shekara 13 fyade

Yan sanda sun kama wani mutumi mai shekaru 29, Soji Ogunrinola, bisa zargin yiwa yarinyar mai shekaru 13 fyade.

Yan sandan jihar Ogun ne suka kama mutumin wanda aka fi sani da bulldozer.

Ya aikata laifin ne a kauyen Ogiri Ojule dake karamar hukumar Odeda na jihar.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Abimbola Oyeyemi, wanda ya tabbatar da lamarin yace kamun nasa ya biyo bayan wani korafi da Monsuru Badmus, mijin mahaifiyar yarinyar yayi a ofishin yan sanda na Odeda cewa mai laifin yayiwa yarinyar da taje hutu kauyen fyade.

Mai karan ya fadama yan sanda cewa wanda ake zargin yayi barazanar kashe yarinyar idan ta fadama wani abunda yayi mata.

An kama wani mutumi bisa zargin yiwa yar shekara 13 fyade

An kama wani mutumi bisa zargin yiwa yar shekara 13 fyade

Yace mahaifiyar yarinyar taga jini a jikin kayan yarinyar wanda hakan yasa ta tambayeta akan abunda ta gani.

KU KARANTA KUMA: Mutane 7 ne suka mutu yayinda 12 suka jikkata a harin da aka kai masallacin Bama

Sai yarinyar tayima mahaifiyarta bayan in dukkanin abun da ya faru.

Yace yanzu haka an kama mai laifin inda daga bisani ya amsa laifinsa.

Mista Oyeyemi yace an dauki yarinyar zuwa asibitin tarayya dake Abeokuta, domin duba lafiyarta.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel