Babu ruwa na : Ban sa hannu wajen dakatar da Ndume ba – Omo Agege

Babu ruwa na : Ban sa hannu wajen dakatar da Ndume ba – Omo Agege

- Sanata Agege ya bayyana yadda aka dakatar da Ndume daga Majalisa

- Agege yace Sanatocin PDP aka yi amfani da su aka dakatar da Sanatan

- Sanatan APC 1 kacal ne ya yarda da matakin da aka dauka kan Ndume

Sanata Ovie Omo-Agege wanda aka dakatar daga Majalisa na kwanaki ya wanke kan sa daga zargin da yake yawo na cewa yana cikin wanda su ka sa hannu aka dakatar da Sanata Ali Ndume kwanakin baya.

Babu ruwa na : Ban sa hannu wajen dakatar da Ndume ba – Omo Agege

'Yan PDP Saraki yayi amfani da su ya dakatar da Ndume inji Agege

Ovie Agege yayi wannan karin haske ne a karshen makon jiya bayan ya ji ana cewa alhakin Ndume ne ya bi shi har aka dakatar da shi ma daga Majalisar. Sanatan yace duk da yana cikin kwamitin da su ka bincike Ndume, bai yi na’am da dakatar da shi ba.

KU KARANTA : Sanatocin APC za su yi fito-na-fito da Saraki a kan Omo Agege

Agege yace da shi da sauran 'Yan uwan sa na APC ba su cikin wadanda su ka sa hannu aka dakatar da Sanata Ali Ndume na Borno. Omo Agege yace mutane 7 ne kurum cikin su 13 su ka sa hannu wajen dakatar da Sanatan wanda mutum 6 ‘Yan PDP ne.

Sanata Agege yace Tayo Alasoadura ne kurum Sanatan APC da ya biyewa ‘Yan PDP. Sanatocin PDP da su kayi kutun-kutun wajen dakatar da Ndume sun hada da : Samuel Anyanwu, Mao Ohuabunwa, Peter Nwaoboshi, Jerimiah Useini, Obinna Ogba da Mathew Urhoghide.

Dama kun ji cewa wani Sanata a kasar yace ba za su yarda da dakatar da Sanatan su watau Omo Agege da aka yi ba ko da dai ba su da shirin taba Bukola Saraki saboda irin goyon-bayan da yake da shi daga Sanatocin PDP.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel