Mutane 7 ne suka mutu yayinda 12 suka jikkata a harin da aka kai masallacin Bama

Mutane 7 ne suka mutu yayinda 12 suka jikkata a harin da aka kai masallacin Bama

Akalla masu bauta 7 ne suka mutu sannan goma sha biyu suka jikkata a yayinda yan kunar bakin wake suka kai hari wani masallacin Bama a safiyar Lahadi, inji wata majiya.

Majiya daga hukumar bayar da agajin gaggawa tace a yanzu haka wadanda suka ji rauni na samun kulawar likita a asibitin Bama.

"Zuwa yanzu dai yan farar hula biyar ne suka mutu a take amma da dama sunji mummunan rauni. Don haka mun kira hukumar bayar da agajin gaggawa muna kuma sanya ran zasu zo su kwashi wadanda suka ji rauni zuwa Maiduguri.” Tawagar hukumar suka fadama majiyarmu ta wayar tarho.

Mutane 7 ne suka mutu yayinda 12 suka jikkata a harin da aka kai masallacin Bama

Mutane 7 ne suka mutu yayinda 12 suka jikkata a harin da aka kai masallacin Bama

Garin Bama na tsawon kilomita 76 daga Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

KU KARANTA KUMA: Satar sandar girma ta majalisa rahama ce a lullube - Sanata

Aranar Lahadi, 22 ga watan Afrilu ne wasu yan kunar bakin wake suka kaiwa massalata hari a wani masallaci dake garn Bama, jihar Borno.

Wannan ba shine karo na farko da suke kaddamar da irin wadannan hare-hare a masallatai ba.

Idan zaku tuna kwanakin baya Legit.ng ta kawo cewa wasu yan gudun hijira sun koma Bama a watan da ya gabata.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel