Sanatocin Buhari za su yi fito-na-fito da Saraki a kan dakatar da Omo Agege

Sanatocin Buhari za su yi fito-na-fito da Saraki a kan dakatar da Omo Agege

- Sanaocin da ke tare da Buhari za su kalubalanci Majalisa

- Kwanaki aka dakatar da wani jigo a Majalisar Omo Agege

- Wasu ‘Yan Majalisan kasar sun ce sam ba za su yarda ba

Mun samu labari daga Jaridar Punch cewa Sanatocin da ke goyon Shugaban kasa Muhammadu Buhari na kokarin ganin yadda za su yi su takawa Bukola Saraki burki a Majalisar Dattawan kasar a makon nan

Sanatocin Buhari za su yi fito-na-fito da Saraki a kan dakatar da Omo Agege

Omo Agege yana cikin 'Yan a-mutun Buhari a Majalisa

Majiyar mu ta bayyana mana cewa ‘Yan Majalisan da ke karkashin lemar Shugaba Buhari sun fara shirin kalubalantar dakatar da ‘Danuwan su da aka yi a Majalisar. Kwanakin baya Majalisa ta dakatar da Sanatan na APC Omo Agege.

KU KARANTA: Sanatan Sokoto Wammako yace shi ba mai kudi bane

Tun a makon da ya wuce dai ‘Yan Majalisar su kayi shirin bore ga Shugancin Saraki na dakatar da babban Sanatan. Sai dai kuma a makon jiyan ne wasu tsageru da ake zargi da sa hannun shi Sanata Agege su ka kutso cikin Majalisar.

Wani Sanata a kasar Yarbawa yace ba za su yarda da dakatar da Sanatan su da aka yi ba ko da dai ba su da shirin taba Bukola Saraki sdaga kujerar sa aboda irin goyon-bayan da yake da shi daga Sanatocin Jam'iyyar adawa na kasar na PDP.

Ba shakka dai a gobe ayi fito-na-ftto da Bykola Saraki bisa dukkan alamu. Kwanaki da aka yi zama dai Saraki yayi tafiya zuwa wani taro a Amurka.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel