ASUU ta bayyana damuwar ta na rashin aikin yi a kasar nan

ASUU ta bayyana damuwar ta na rashin aikin yi a kasar nan

- Kungiyar malaman jami'a ta nuna damuwarta akan rashin aikin mutane miliyan 16 wadanda aka yaye

- A ranar lahadi ne Kungiyar malaman jami'a (ASUU) ta nuna rashin Jin dadinta na rashin aikin miliyan 16 na wadanda aka yaye da kuma miliyan 12 na wadanda suka bar karatun

- Kungiyar tayi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya duba rayuwar wadanda abin ya shafa kuma ya fitar dasu daga cikin wadanda ake kira 'yan zaman kashe wando da cima zaune

ASUU ta bayyana damuwar ta na rashin aikin yi a kasar nan

ASUU ta bayyana damuwar ta na rashin aikin yi a kasar nan

Shugaban ASUU na jami'ar Ibadan, Dr Deji Omole wanda ya fadi hakan a ranar lahadi a Ibadan ya kara da cewa ya zama dole a tunatar da minista cewa bai kamata a yi wasa da rayuwar yaran talakawa ba a siyasa, kuma da mamakin cewa niyyar taimakon gaggawa da aka shirya a bangaren ilimi ba a zartar ba.

ASUU tace abin haushi ne ace gwanatin da ta kasa bada damar samun ingantaccen ilimi ita ce take Kiran samari zauna gari banza da Cima zaune.

"Me Gwamnatin tayi don ceto yara miliyan 12 da suka bar karatu a Najeriya? Wanne shirin gwamnati take yi don magance matsalar aikin yi mutane miliyan 16 da jami'o'i suka yaye? Wanne tanadi gwamnatin take ma samarin da suke bautawa kasa su gama babu aikin yi ko jari? In gwamnati ta kasa tallafawa samarin, zasu kuwa zama tashin hankali ga kasar nan gaba".

DUBA WANNAN: Hadari ya rutsa da iyayen Chibok

ASUU ta tunawa ministan ilimi alkawarin da akayi na tallafin gaggawa ga bangaren ilimi a watan Afirilun wannan shekarar domin farfado da ingancin ilimin da yan'kasar ke samu.

A baya dai shugaba Buhari ya kira daukacin samarin Najeriya malalata masu neman na bati, lamari da ya bakantawa samarin rai suka far masa da kushiya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel