Talakawa sun gaji da gafara sa basu ga kaho ba: Miliyoyin 'Yan Najeriya sun ki zuwa karbar katin zabe

Talakawa sun gaji da gafara sa basu ga kaho ba: Miliyoyin 'Yan Najeriya sun ki zuwa karbar katin zabe

A ranar Lahadin nan ne wani Dan Majalisa, a jihar Legas, Mista Setonji David, yace zai saka masu sanarwa su shiga gari domin su wayar da kan al'ummar mazabarsa, sannan su nuna musu muhimmancin yin katin zabe

Talakawa sun gaji da gafara sa basu ga kaho ba: Miliyoyin 'Yan Najeriya sun ki zuwa karbar katin zabe

Talakawa sun gaji da gafara sa basu ga kaho ba: Miliyoyin 'Yan Najeriya sun ki zuwa karbar katin zabe

A ranar Lahadin nan ne wani Dan Majalisa, a jihar Legas, Mista Setonji David, yace zai saka masu sanarwa su shiga gari domin su wayar da kan al'ummar mazabarsa, sannan su nuna musu muhimmancin yin katin zabe.

David, wanda ke wakiltar mazabar Badagry II, dake jihar Legas a karkashin jam'iyyar APC mai mulki, ya fada wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya, a yanzu haka akwai katin zabe na kimanin mutane Miliyan daya da rabi wadanda basu zo sun karba ba har yau a fadin jihar.

A rahoton da hukumar ta bayar a watan Maris din wannan shekarar ya nuna cewar jihar Legas ita ce take dauke da mafi yawan wadanda basu je sun karba katin zaben nasu ba, inda suke da kimanin mutane 1,401,390; sai kuma jihar Oyo da take biye mata da mutane 647,586; da jihar Edo 449,001; inda ita kuma jihar Kano take da mutane 195,941.

DUBA WANNAN: Matsalar tsaro: Buhari zai hada taron gaggawa

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta ce har yanzu da akwai katin zabe na mutum 7,920,129 da ba a karba a fadin kasar nan.

Dan Majalisar ya ce abin takaicine ace mutane sun cire sha'awar yin zabe a zuciyar su, inda har ace kimanin mutane miliyan 1.4 basu karbi katin su ba a jihar Legas. Ina yin iya bakin kokarina a mazabata domin ganin mutane sun zo sun karbi katin su, har na saka masu sanarwa domin a wayar da kan al'umma.

"Za mu kuma tabbatar da cewar mun ƙarfafa musu gwiwa ta hanyar samar da ababen hawa don su kai su ofishin INEC.

"Muna yin iya bakin kokarin mu don nunawa mutane su san dalilin da ya sa suke bukatar samun katin zaben kuma meya sa yake da mahimmanci a gare su suyi aiki da su.

''Ta haka ne, za su iya zabar mutanen da suke so su wakilce su a cikin gwamnati." inji shi.

Ko a baya ma dai, an saba samun aringizon kuri'u wadanda aka kada da kuri'un jama'a da basu zo zabe ba, wasu lokuta kuma, takarsun dangwalawar da suka rage, su ake amfani dasu, muddin babu jama'a da yawa da suka fito kada kuri'un zaben.

A zabukan jihar Kano na kananan hukumomi ma, an sami kananan yara da suka dangwala kuri'u, amma huumar zaben ta karyata hakan duk da cewa shaidun gani da ido da hotuna sun nuna a zahiri hakan ya faru.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel