Gwamnatin tarayya ta bayyana yadda zata kashe miliyan $322.5 kudin Abacha da ta karbo

Gwamnatin tarayya ta bayyana yadda zata kashe miliyan $322.5 kudin Abacha da ta karbo

Gwamnatin tarayya ta kara karbo wasu daga cikin kudin da Abacha ya ajiye a bankunan kasashen ketare da yawan su ya kai dakar Amurka miliyan US$322,515,831.83.

A wata tattaunawar hadin gwuiwa da suka yi da manema labarai a birnin Washington DC na kasar Amurka inda suka halarci taron kasa da kasa a kan bunkasa harkokin tattalin arziki, Ministar kudi uwargida Kemi Adeosun da babban gwamnan bankin kasa, Godwin Emefiele, sun tabbatar da shigar kudin asusun Najeriya dake babban bankin kasa (CBN) daga gwamnatin kasar Swiss.

Adeosun ta ce gwamnati zata yi amfani da kudin ne wajen tabbatar da cigaba mai dorewa ga tattalin arzikin Najeriya.

Gwamnatin tarayya ta bayyana yadda zata kashe miliyan $322.5 kudin Abacha da ta karbo

Adeosun da Emefiele

Ta kara da cewar gwamnati zata cigaba da bunkasa lallitar ta a yayin da ake cigaba da samun saukin hauhawar farashin kayan masarufi.

A cewar Adeosun, zuwa shekara mai zuwa, 2019, tattalin arzikin Najeriya zai kara bunkasa da habaka matukar sun bi tsarin da suka yi na farfado da tattalin arzikin Najeriya.

DUBA WANNAN: Auren jinsi: Buhari ya mayar wa da Firaministar Ingila martani

A nasa jawabin, Emefiele, ya bayyana cewar asusun Najeriya dake ketare ya kai US$47.93 tare da kara bayyana cewar ya zama dole mu cigaba da tsimi da tanadi domin gujewa irin halin da tattalin arzikin Najeriya ya shiga sakamakon kuskuren gwamnatin baya na gaza adana dumbin kudi da gwamnati ta samu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel