'Yan bindiga sun ci karen su ba babbaka a jihar Kogi, sun kashe mutane fiye da 10 da kuma kona gidaje

'Yan bindiga sun ci karen su ba babbaka a jihar Kogi, sun kashe mutane fiye da 10 da kuma kona gidaje

- Har yanzu yan bindiga na cigaba da tabka barna son ransu

- A yau ma sun ragargaji wani gari suka kuma tafi abinsu

Da safiyar jiya Lahadi ne wasu 'yan bindiga suka kai hari a wasu yankuna biyu dake karamar hukumar Bassa a jihar Kogi, lamarin da ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutane sama da shida.

'Yan bindiga sun ci karen su ba babbaka a jihar Kogi, sun kashe mutane fiye da 10

'Yan bindiga sun ci karen su ba babbaka a jihar Kogi, sun kashe mutane fiye da 10

Sai dai wani rahoton baya-bayan nan ya tabbatar da adadin wadanda suka rasa rayukan nasu ya kai mutum 10.

Basaraken yankin Mozum dake Bassa, Khalid Bukar, ya shaidawawa manema labarai a Lokoja cewa, farmakin ya dau tsawon lokaci har zuwa bayan Azahar din ranar Lahadin.

Yace 'yan bindigar sun ruguza gidajen mutane da dama a yankin tare da harbe wasu mutane biyar nan take.

KU KARANTA: Aiki sai Maza: Sojoji sunyi nasarar dakile hari daga ƴan Boko Haram

Basaraken ya kara da cewa, ya yi gaggawar sanar da 'yan sanda lamari sai dai a lokacin sun yi barna kafin zuwan 'yan sandan.

A ta bakin mai magana da yawun hukumar 'yan sandan jihar Kogi, William Aya, ya ce sun sami nasarar harbe maharan shida, ba biyar ba kamar yadda aka sanar da farko. Ya kara da cewa, sama da gidaje 15 ne 'yan bindigar suka lalata a yankin Kpanchi.

'Yan bindiga sun ci karen su ba babbaka a jihar Kogi, sun kashe mutane fiye da 10

'Yan bindiga sun ci karen su ba babbaka a jihar Kogi, sun kashe mutane fiye da 10

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel