EFCC: Tsohon Gwamnan Sokoto Wammako yace bai taba rike Biliyan 1 ba
- Aliyu Wammako ya karyata rade-radin ya saci kudi yana Gwamna
- Tsohon Gwamnan yace shi fa bai taba satar kudin Jihar Sokoto ba
- Yanzu haka yace alakar sa da Shugaba Buhari tana da kyau kwarai
Mun samu labari daga Jaridar Daily Trust cewa Tsohon Gwamnan Sokoto Aliyu Magatakarda Wammako ya karyata rade-radin da ke yawo cewa yayi awon gaba da kudin Jihar Sokoto lokacin yana Gwamna a Gwamnatin baya.
Ana zargin tsohon Gwamnan na Sokoto da kuma takwaran sa tsohon Gwamnan Jihar Kano Rabi’u Musa Kwankwaso wadanda yanzu duk Sanatoci ne da cewa sun saci kudin da ya haura Naira Biliyan 18 a lokacin sun a ofis.
Aliyu Wammako wanda shi ne ‘Dan Majalisar Arewaci Sokoto a Majalisar Dattawa yace bai taba ganin Biliyan 1 ba a Duniya. Tsohon Gwamnan yace labaran da ake yadawa na cewa ya saci wadannan kudi ba gaskiya bane.
KU KARANTA: Shugaba Buhari ya dawo gida da tsaraba daga Ingila
Sanatan Kasar yace wasu ne kurum ke yada wannan labarai na kage amma ba Hukumar yaki da cin hanci bane ke zargin sa inda ya kalubalanci a kawo hujja a kan sa. Wammako yace shi ba mai kudi bane don ba ya adana dukiya.
Haka kuma dai tsohon Gwamnan ya karyata cewa ya samu sabani da Shugaban kasa Buhari, yace alakar sa da Shugaban kasar sai ma godiya. Dama dai kun ji cewa ana zargin Sanatocin 2 da laifin sata.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng