Zaben 2019: Kungiyar magoya bayan Atiku za ta yi babban gangamin a jihar Legas

Zaben 2019: Kungiyar magoya bayan Atiku za ta yi babban gangamin a jihar Legas

Wata kungiya ta 'yan Najeriya masu ra'ayin dan takarar shugaban kasar Najeriya a zaben 2019 mai suna Re-building Nigeria Initiativeta a turance ayyana cewa ta shirya tsaf domin kaddamar da gangamin yakin neman zaben gwanin su a jihar Legas ranar Lahadi mai zuwa 22 ga watan Afrilu.

Mataimakin shugaban kungiyar na kasa baki daya Earnest Fasan shine ya kwarmatawa manema labarai hakan a garin na Legas inda kuma ya ce hakan na a matsayin wata 'yar manuniya ce ga wasu tarukan daban domin samun nasarar gwanin na su.

Zaben 2019: Kungiyar magoya bayan Atiku za ta yi babban gangamin a jihar Legas

Zaben 2019: Kungiyar magoya bayan Atiku za ta yi babban gangamin a jihar Legas

KU KARANTA: Ingila ta ba Buhari Fam miliyan 1

A wani labarin kuma, Hukumar nan ta gwamnatin tarayya dake yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ta bayyana cewa zata fara binciken da ya kamata game da takardar korafin da suka samu na zargin badakalar ma'aikatan bogi da hadimi da kuma matar shugaban majalisar dattijai ke ciki.

Mai magana da yawun hukumar ta EFCC Mista Wilson Uwajaren shine ya sanarwa da wakilin majiyar mu hakan a wata tattaunawar da sukayi ta wayar tarho da yake neman karin bayani.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel