Tsarabar Ingila: Gwamnatin Ingila ta ba Buhari Fam miliyan 1 don yakar Boko Haram

Tsarabar Ingila: Gwamnatin Ingila ta ba Buhari Fam miliyan 1 don yakar Boko Haram

Gwamnatin kasar hadaddiyar daular Ingila ta yi alkawarin baiwa kasar Najeriya karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari kayayyakin zamani na yakar 'yan ta'addan Boko Haram da suka kai na darajar Fam miliyan daya.

Babban ministan kasar Ingila din ne dai na fannin tsoji Mista Mark Lancaster ya sanar da hakan yayin tattaunawar sa da takwaran sa na tsaron Najeriya Mansur Dan-Ali a birnin Landan din.

Tsarabar Ingila: Gwamnatin Ingila ta ba Buhari Fam miliyan 1 don yakar Boko Haram

Tsarabar Ingila: Gwamnatin Ingila ta ba Buhari Fam miliyan 1 don yakar Boko Haram

KU KARANTA: Mata ta gari: Dan shekara 108 ya bayyana sirrin tsawon rayuwa

Legit.ng dai ta kara da samun haka zalika cewa Mista Mark ya ce wannan kadan ne daga cikin gudummuwar da kasar ta sa za ta ba Najeriya domin ganin an murkushe ayyukan ta'addanci.

A wani labarin kuma, Wata 'yar shekara 16 a duniya kacal 'yar asalin kasar Najeriya amma wadda ke zaune a kasar tarayyar Amurka mai suna Oluwatofunmi Oteju ta kwashi 'yan kallo bayan da ta lashe kyautar 'shugaba' ta shekara a jami'ar Augsburg.

Kamar dai yadda muka samu daga majiyar mu, Oluwatofunmi an karramata ne a ranar Lahadin da ta gabata domin kara mata karfin gwuiwa akan ficen da tayi a wani darasi kan shugabanci.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel