Yanzu-yanzu: Boko Haram sun kai harin bam masallaci, sun kashe mutane da dama

Yanzu-yanzu: Boko Haram sun kai harin bam masallaci, sun kashe mutane da dama

A kalla mutane biyar ne suka mutu a wani hari da Boko Haram suka kai wani masallaci a jihar Borno.

Masu ibada da dama sun sama raunuka a harin bam din da aka kai da misalin karfe 5:30 na safiya a garin Bama.

Ali Abacha, wani jami'in hukumar tsaro ta NSCDC ya tabbatar da afkuwar lamarin ga jaridar The Cable.

Abacha ya ce wasu mata ne guda biyu suka kai harin na kunar bakin wake ta hanyar yin sumame zuwa ciki masallacin yayin da jama'a ke gudanar da sallar Asuba.

Yanzu-yanzu: Boko Haram sun kai harin bam masallaci, sun kashe mutane da dama

Harin bam din jami'ar Maiduguri

"Mun ji kara mai karfi yayin da muke gabatar da sallah. Karar mai karfi ce sosai, hakan ya tabbatar mana da cewar wani abu maras dadi ya faru.

Mun samu gawar mutanen da dama bayan mun isa wurin," in ji Kachala.

DUBA WANNAN: Rashin tausayi: Kalli jaririn da aka tsinta cikin kwata a Kano

An garzaya da wadanda suka samu raunuka zuwa asibitin garin Bama yayin da wadanda suka mutu kuma aka iya gane fuskokin su aka mika su ga iyalan su domin yi masu jana'iza.

An bude hanyar Maiduguri zuwa Bama da aka rufe da aka rufe tun 2014 a watan Maris na wannan shekarar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel