Manyan shari’ar da aka yi da Gwamnan Kaduna El-Rufai daga 2015 zuwa yau

Manyan shari’ar da aka yi da Gwamnan Kaduna El-Rufai daga 2015 zuwa yau

Daga hawan Malam Nasir El-Rufai kujerar Gwamna zuwa yanzu an yi ta fama shari’a da shi iri-iri. Jiya ma dai kuma Gwamnan yace zai maka wani a Kotu saboda jifan da yayi da sharri. Sai dai wasu na ganin shi ma Gwamnan yayi irin wannan aika-aika a lokacin yana ‘Dan adawa.

Ga wasu daga cikin shari’ar da aka yi da Gwamnan na Jihar Kaduna:

Manyan shari’ar da aka yi da Gwamnan Kaduna El-Rufai daga 2015 zuwa yau

An shiga Kotu da El-Rufai ya fi a kirga daga hawan sa Gwamna

1. Shari’ar kujerar Gwamna

Bayan hawan Gwamna Nasir El-Rufai mulki ne Jam’iyyar adawa ta maka shi Kotu tana kalubalantar zaben da ya lashe. Bayan nan shari’ar ta kai har Kotun daukaka kara inda Gwamnan yayi nasara a karshen 2015.

2. Shari’ar Gwamna da masu gari

Wata Kotu a Kafanchan ta dakatar da Gwamna El-Rufai da sallamar Dagatai da Lawalai da Masu Unguwanni sama da 4000 a Jihar bayan an maka shi kara a farkon bana. Sai dai duk da haka an sallame masu garin daga aiki.

KU KARANTA: Jirgin Shugaba Buhari ya kai kasar Inyamurai

3. Shari’ar sa da Audu Maikori

A karshen 2017 Gwamna Nasir El-Rufai yayi shari’a da wani bawan Allah mai suna Audu Maikori inda har ta kai Kotu ta nemi Gwamnan ya biya wannan mutumi makudan kudi har Naira Miliyan 40 a dalilin wahalar da shi da yayi.

4. Shari’ar sa da Malaman Makaranta

Haka-zalika, ‘Yan kwadago sun maka Gwamnan na Jihar Kaduna a Kotu domin a tsaida yunkurin da yake yi a lokacin na sallamar Malaman makaranta sama da 20, 000. A Disamban 2017 Kotu ta nemi Gwamnan ya dakata amma yayi kunnen kashi.

5. Zaben kananan Hukumomi

A Disamban 2016 ne wani babban Kotu ya soke Kantomomin da Gwamna El-Rufai ya nada a kananan Hukumomi 23 aka kuma nemi ayi sabon zabe. Yanzu dai an sa ranar zaben a wata mai zuwa.

Bayan nan Gwamna Nasir El-Rufai ya shiga Kotu fiye da sau daya da 'Yan Kungiyar IMN ta shi'a daga 2015 bayan an damke Sheikh Ibrahim Zakzaky. Haka kuma Gwamnan ya maka Yusuf Datti Ahmed a Kotu saboda ci masa mutunci da yayi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel