Aiki sai Maza: Sojoji sunyi nasarar dakile hari daga ƴan Boko Haram

Aiki sai Maza: Sojoji sunyi nasarar dakile hari daga ƴan Boko Haram

- Aiki ga mai kare ka, Sojoji na cigaba da yunkurin ganin karshen Boko Haram gaba daya

- An gabza artabu da Sojoji da yan Boko Haram

A jiya Asabar ne sojojin Najeriya suka yi nasar dakile yunkurin ƴan ta'addan Boko Haram na kai hari garin Gamboru-Ngala a jihar Borno.

Kakakin rundunar Brig.-Gen. Texas Chukwu, ya bayyana cewa an kashe ƴan Boko Haram din da dama wasu kuma suka tsere.

Aiki sai Maza: Sojoji sunyi nasarar sake dakile hari daga ƴan Boko Haram

Aiki sai Maza: Sojoji sunyi nasarar sake dakile hari daga ƴan Boko Haram

"Jami'anmu na bataliya ta 3 na dakarun Lafiya dole sun samu nasarar dakile harin da ƴan Boko Haram suka kai Gamborun-Ngala" Kakin ya bayyana.

KU KARANTA: Kun jawowa Najeriya asara, Sarki Sanusi II ya caccaki ministocin Buhari

"Mun kama guda daga cikinsu yayinda ragowar suka gudu sakamakon lugudan wuta da muka musu, sai dai kuma tsautsayi yasa mun rasa Sojanmu guda a artabun" Chukwu ya shaida.

Sannan ya kuma ce, "Dakarun sun samu nasarar kwace muggan makamai daga wurin ƴan Boko Haram ɗin waɗanda suka haɗa da; Babbar bindiga mai charbi da bindigar kakkaɓo jirgi da AK 47 biyu da sauransu".

Kakakin Sojojin ya kuma buƙaci jama'a da su cigaba da bawa rundunar haɗin kai a koda yaushe tare da kai rahoton duk wani abu da basu yarda da shi ba ga jami'an tsaro.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel