Mu hadu a Kotu: El-Rufai ya fadawa wani mutumi da yayi masa kage

Mu hadu a Kotu: El-Rufai ya fadawa wani mutumi da yayi masa kage

- Gwamnan Jihar Kaduna yace zai maka wani Talakan sa a gaban Alkali

- Gwamnan yace tun farko ma dai wannan Bawan Allah ya shiryawa zama

- El-Rufai yace wannan mutumi yayi masa sharrin da zai bara masa suna

Jiya ne mu ka ji cewa Gwamnan Jihar Kaduna watau Malam Nasir El-Rufai ya shirya maka wani Talakan sa a Kotu dalilin zargin yi masa sharri a shafin sada zumunta na Tuwita. Gwamnan yace ya shirya zama gaban Alkali.

Mu hadu a Kotu: El-Rufai ya fadawa wani mutumi da yayi masa kage

Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai zai maka wani mutumi a Kotu

Stephen Kefas wani Bawan Allah yayi amfani da shafin sa na Tuwita inda ya zargi Gwamnan Jihar da tada wutar da ta ci Hukumar zabe na Jihar watau SIECOM. A cewar Kefas Gwamnan nan ne da kan sa ya jawo gobarar.

Kamar yadda mu ka samu bayani daga Tuwita, Kefas yace Gwamna El-Rufai ya kona ofishin ne saboda ba ya so ayi zaben kananan Hukumomi a watan gobe. Gwamnan Jihar dai bai dauki wannan magana da wasa ba sam.

KU KARANTA: Yadda Jonathan yake yabon samarin Najeriya lokacin kamfe

Gwamnan ya bayyanawa wannan mutumi cewa kalaman sa za su iya bata masa suna don haka ya shirya ganin sammaci daga Kotu domin ya kare kan sa. Gwamnan yace tun wuri ma dai Kefas din ya bayyana adireshin sa.

Ba dai yau Gwamnan ya saba maka Jama'a a Kotu ba. Haka kuma idan ba ku manta ba dai ana sa rai za ayi zaben kananan Hukumomin Jihar Kaduna ne a 12 ga watan Mayun gobe. Tuni dai aka yi zaben fitar da gwani na Jam’iyyu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel