Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya dawo daga Landan

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya dawo daga Landan

Labarin da ke shigowa yanzun nan na nuna cewa shugaba Muhammadu Buhari ya iso Najeriya daga kasar Landan inda ya tafi kimanin makonni biyu yanzu.

Shugaba Buhari ya tafi kasar Birtaniya ranan Litinin, 9 ga watan Afrilu 2018 bayan ya alanta niyyar takaransa a zaben 2019 a ganawar da yayi da masu ruwa da tsakin jam'iyyar APC a Abuja.

Shugaban kasan ya tafi ne domin halartan taron shugabannin kasashen Commonwealth da aka gudanar a birnin Landan.

KU KARANTA: Hanyoyi 4 da jam'iyyar adawa ta PDP zata bi don ganin ta kwace mulki a 2019

A kwanakin da yayi a Landan, shugaba Buhari ya gana da Firam ministan Birtaniya, Theresa May, inda ya tattuna da ita kna al'amuran da ya shafi alakar Najeriya da Birtaniya da kuma abinda gwamnatinsa ke yi.

Kana ya gana da faston Canterbury, jagoran matasan Najeriya a Landan, jigon jam'iyyar APC, Bola Tinubu, da sauransu.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel