Zaben 2019: Hukumar INEC ba za ta yi ma mu adalci ba - Secondus

Zaben 2019: Hukumar INEC ba za ta yi ma mu adalci ba - Secondus

Shugaban babbar jam'iyyar adawa ta PDP, Mista Prince Uche Secondus a jiya ya kwarmatawa tawagar tarayyar kasashen Turai da suka kai masa ziyara a ofishin sa cewa tuni jam'iyya mai mulki ta APC ta kammala hada baki da hukumar zabe ta INEC domin yin murdiya a zaben 2019 mai zuwa.

Mista Secondus dai ya yi wannan ikirarin ne lokacin da tawagar kungiyar kasashen ta tarayyar Turai karkashin jagorancin Ketil Karlsen suka kai masa ziyarar ban girma a babbar Sakatariyar jam'iyyar.

Zaben 2019: Hukumar INEC ba za ta yi ma mu adalci ba - Secondus

Zaben 2019: Hukumar INEC ba za ta yi ma mu adalci ba - Secondus

KU KARANTA: Dalilin da ya sa 'yan majalisu ke da bakin jini a wajen talakawa

Legit.ng ta samu cewa Mista Secondus ya kuma bayyana cewa su tuni jam'iyyar su ta fidda rai ga samun damar shiga zabe sahihi a kasar nan.

A wani labarin kuma, Wani ayarin matasa dake kyautata zaton 'yan daba ne sun yi shigar burtu sannan suka farwa babbar Sakatariyar jam'iyyar APC mai mulki a garin Umuahia, babban birnin jihar Abia dake a shiyyar kudu maso gabashin Najeriya tare kuma da yin awon gaba da wasu dumbin kudade.

Da yake tsokacin game da lamarin, mai magana da yawun jam'iyyar a jihar Mista Donatus Nwamkpa ya zargi wasu jiga-jigan jam'iyyar su biyu a jihar watau Ikechi Emenike da kuma Emmanuel Ndukwe da laifin jagorantar 'yan daban.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel