Dalilin da yasa 'yan majalisa ke da bakin jini ga talakawa - Sanata Musa

Dalilin da yasa 'yan majalisa ke da bakin jini ga talakawa - Sanata Musa

Sanata Ibrahim Musa, da ke zaman dan majalisar dattijai da ke wakiltar mazabar jihar Neja ta yamma ya alakanta rashin wayewa a siyasance a matsayin babban dalilin da ya sa 'yan majalisa a Najeriya suke da matukar bakin jini ga talakawa.

Da yake ganawa da majiyar mu, Sanata Ibrahim Musa ya bayyana cewa har yanzu talakawa basu gama fahimtar ainihin aikin dan majalisa ba shi yasa ma da mutum ya ci zabe za kaga al'umma na tururuwa wajen sa domin ya yaye masu matsalar da ta dame su.

Dalilin da yasa 'yan majalisa ke da bakin jini ga talakawa - Sanata Musa

Dalilin da yasa 'yan majalisa ke da bakin jini ga talakawa - Sanata Musa

KU KARANTA: Hanyoyi 4 da jam'iyyar PDP za ta bi don kada Buhari a 2019

Legit.ng ta samu Sanata ya kara da cewa maimakon a bar 'yan majalisar suyi aikin yin doka da kuma sa ido ga bangaren zartaswa, mutanen sun kwammace su rika raba masu kudi wanda kuma ba su da su.

A wani labarin kuma, Jami'ar nan budaddiya mallakin gwamnatin tarayya watau National Open University of Nigeria (NOUN) ta mika shaidar kammala karatun digiri na daya da na biyu zuwa ga wasu 'yan Najeriya dake zaman gidan yari na Kirikiri a jihar Legas.

A yayin bikin mika takardar shaidar, mataimakin shugaban jami'ar Farfesa Abdallah Adamu ya kuma bayyana cewa 'yan gidan yarin sun nuna kwazo matuka sannan kuma yayi masu addu'ar cin gajiyar karatun da suka yi.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel