Hanyoyi 4 da jam'iyyar adawa ta PDP zata bi don ganin ta kwace mulki a 2019

Hanyoyi 4 da jam'iyyar adawa ta PDP zata bi don ganin ta kwace mulki a 2019

Hakika dai tuni masu lura da al'amurran yau da kullum suka yi amannar cewa an kada gangar siyasar zabukan game gari na 2019 mai zuwa musamman ma dai duba da yadda harkokin siyasar suke ta kara daukar zafi.

Sai dai kuma wannan yanayin shine irin sa na farko da jam'iyyar adawa ta PDP ta tsinci kanta a ciki tun dawowar harkokin siyasa a shekarar 1999 musamman ganin cewa yanzu suna yin adawa ne.

Hanyoyi 4 da jam'iyyar adawa ta PDP zata bi don ganin ta kwace mulki a 2019

Hanyoyi 4 da jam'iyyar adawa ta PDP zata bi don ganin ta kwace mulki a 2019

KU KARANTA: Ofishin hukumar zaben jihar Kaduna ya kama da wuta

Wannan ne ma ya sanya jam'iyyar take ta fadi-tashin ganin ta sake yunkurowa domin ta kwace kambun mulkin daga hannun jam'iyyar APC a zaben mai zuwa.

Yanzu haka dai shugabannin jam'iyyar da ma sauran jiga-jigan ta na ta aiki tukuru ne domin ganin hakar ta su ta cimma ruwa.

Ga wasu daga cikin hanyoyin da ake ganin idan jam'iyyar ta PDP ta bi to za ta iya lashe zaben mai zuwa na 2019:

1. Canza suna

2. Zawarcin 'yan siyasa daga sauran jam'iyyu

3. Neman hadewa da wasu jam'iyyun domin su kara karfi

4. Gudanar da sahihan zabukan fidda gwani

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel