Da dumin sa: 'Yan daba sun far wa Sakatariyar jam'iyyar APC, tare da tafka uwar sata a wannan jihar

Da dumin sa: 'Yan daba sun far wa Sakatariyar jam'iyyar APC, tare da tafka uwar sata a wannan jihar

Wani ayarin matasa dake kyautata zaton 'yan daba ne sun yi shigar burtu sannan suka farwa babbar Sakatariyar jam'iyyar APC mai mulki a garin Umuahia, babban birnin jihar Abia dake a shiyyar kudu maso gabashin Najeriya tare kuma da yin awon gaba da wasu dumbin kudade.

Da yake tsokacin game da lamarin, mai magana da yawun jam'iyyar a jihar Mista Donatus Nwamkpa ya zargi wasu jiga-jigan jam'iyyar su biyu a jihar watau Ikechi Emenike da kuma Emmanuel Ndukwe da laifin jagorantar 'yan daban.

Da dumin sa: 'Yan daba sun far wa Sakatariyar jam'iyyar APC, tare da tafka uwar sata a wannan jihar

Da dumin sa: 'Yan daba sun far wa Sakatariyar jam'iyyar APC, tare da tafka uwar sata a wannan jihar

KU KARANTA: Buhari ya baro Landan zuwa Najeriya

A wani labarin kuma, Jami'ar nan budaddiya mallakin gwamnatin tarayya watau National Open University of Nigeria (NOUN) ta mika shaidar kammala karatun digiri na daya da na biyu zuwa ga wasu 'yan Najeriya dake zaman gidan yari na Kirikiri a jihar Legas.

A yayin bikin mika takardar shaidar, mataimakin shugaban jami'ar Farfesa Abdallah Adamu ya kuma bayyana cewa 'yan gidan yarin sun nuna kwazo matuka sannan kuma yayi masu addu'ar cin gajiyar karatun da suka yi.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel