Buhari ya kamo hanyar sa bayan halartar taro a Birnin Landan

Buhari ya kamo hanyar sa bayan halartar taro a Birnin Landan

Mun samu rahoton cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya baro Birnin Landan zuwa Najeriya bayan halartar taron kungiyar shugabannin kasashen Commonwealth da kuma ganawa da Firai Ministan kasar Birtaniya, Theresa May.

Jaridar ta samu wannan rahoto ne da sanadin wani Bidiyo da Bashir Ahmad, babban kadimin shugaban kasa akan sabuwar hanyar sadarwa ya bayyana a shafin sa na sada zumunta.

Shugaba Buhari yayin jawabai a taron Commonwealth a Birnin Landan

Shugaba Buhari yayin jawabai a taron Commonwealth a Birnin Landan

Hadimin ya bayyana cewa ana sa ran shugaba Buhari zai sauka a babban birnin kasar nan na tarayya a Yammacin yau na Asabar.

KARANTA KUMA: Fayose, Obanikoro da Omisore sun yi asarar dukiya ta N2.273b ga hukumar EFCC

Rahotanni sun bayyana cewa, bayan halartar taron shugaba Buhari ya kuma gana da wasu shugabannin kasashe da dama.

A baya jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, shugaban kasar ya kuma gana da wani aminin sa, babban Limamin cocin Canterbury, Justin Welby, akan wasu harkokin tsaro da suka shafi Najeriya.

Kalli Bidiyon yayin da Shugaban Buhari ke bankwana a birnin Landan

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel