Badakalar N10b: Har majalisun kasar nan sun kashe N6.6b daga ciki, cefanen motoci masu tsada suka yi

Badakalar N10b: Har majalisun kasar nan sun kashe N6.6b daga ciki, cefanen motoci masu tsada suka yi

- An bankado badakalar ne da ta kai akalla dala biliyan 10 ta nairori

- Ga alama shugaba Buhari bai ma san an tafka badakalar ba

- Saraki da Dogara sun saya wa 'yan majalisar manyan motoci

Badakalar N10b: Har majalisun kasar nan sun kashe N6.6b daga ciki, cefanen motoci masu tsada suka yi

Badakalar N10b: Har majalisun kasar nan sun kashe N6.6b daga ciki, cefanen motoci masu tsada suka yi

Bayan an manna musu kudin da zasu kashe a shekarar 2018 har naira biliyan 125, hakan bai ishe su ba, banda uban albashi da suke diba daga lalitar gwamnati, sai kuma gashi wai sun amshi wata Naira biliyan goma daga m'aikatar kudi, ko rabin 2018 din ba'a kai ba.

An bankado wannan badakala ne bayan da Sahara Reporters da Premium Times suka sami kishin-kishin din badakalar.

Majalisar dattijai ta kashe N3.2b daga ciki, inda ta sayi motocin kasaita ga Sanatocin ta, ta hannun kamfunnan kwangila na kawo motoci guda 10, wannan kuma na zuwa ne bayan N13m da suke amsa kowanne wata a bankunansu.

DUBA WANNAN: Zawarcin kabilar Igbo a 2019

Majalisar wakilai kuma ta kashe biliyan ukku, itama a motocin daga kamfunna 17, sai ma kuma hannun ma'aikatar majalisar, watau Management da admin, wadanda suka kashe N600m suma a sayen motocin.

MAjalisun dai babu wani abu da suke yi sai wai dokar kasa, surutu, da bacci.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel