Adeosun: Dalili na na baiwa majalisun kasar nan N10b, wannan ba cuwa-cuwa bace

Adeosun: Dalili na na baiwa majalisun kasar nan N10b, wannan ba cuwa-cuwa bace

- An gano badakalar ne bayan da Sahara Reporters ta fasa kwai

- Ministar ta bada dalilanta na mikawa Majalisar kudaden

- Sun kashe sune sun sayi manyan motoci

Adeosun: Dalili na na baiwa majalisun kasar nan N10b, wannan ba cuwa-cuwa bace

Adeosun: Dalili na na baiwa majalisun kasar nan N10b, wannan ba cuwa-cuwa bace

Ministar Kudi, Kemi Adeosun, ta karyata rahoton cewa ta aikata ba daidai ba, kan batun biliyoyin da ta mika wa majalisun kasar nan kawai don su sayi motoci, tace bata san ko ma wadanda suka sakin rahoton, ko sun san yadda ake aikin gwamnati ko aikin jarida ba.

A cewarta dai, ita da Akanta Janar na kasa, Ahmed Idris ne suka mika wa majalisar kudin, kuma duk da kudin baya cikin kasafinsu, tace babu cuwa-cuwa cikin lamarin.

DUBA WANNAN: Zawarcin kabilar Igbo a 2019

Bayan an manna musu kudin da zasu kashe a shekarar 2018 har naira biliyan 125, hakan bai ishe su ba, banda uban albashi da suke diba daga lalitar gwamnati, sai kuma gashi wai sun amshi wata Naira biliyan goma daga m'aikatar kudi, ko rabin 2018 din ba'a kai ba.

Jaridun kasar nan dai sun tona bayanan ne, kuma gwamnatin ta kasa bada wani dalili banda cewa 'cikin-aiki ne aka kashe kudaden'.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel