Ministar kudi Adeosun, da shuwagabannin majalisun kasar nan cikin badakalar biliyan 10

Ministar kudi Adeosun, da shuwagabannin majalisun kasar nan cikin badakalar biliyan 10

- Ana yawan zargin majalisar da cima-zaune da wawaso

- N10b ce aka taras Ministar kudi ta antaya wa shuwagabannin majalisar

- Sun kuma kashe fiye da rabi kan motocinsu ya zuwa yanzu

Ministar kudi Adeosun, da shuwagabannin majalisun kasar nan cikin badakalar biliyan 10
Ministar kudi Adeosun, da shuwagabannin majalisun kasar nan cikin badakalar biliyan 10

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace Dole ne yayi kokarin hana mahukuntan siyan motocin alfarma da kudin da ba nasu ba duk da halin da kasar take ciki.

Majalisar dattawa ta bada Naira biliyan 6.6 don siya ma dattawan motocin alfarma, PREMIUM TIMES da UDEME su suka bada rahoton yau. Bayani ya nuna cewa majalisar ita tafi kowa kashe kudi, siyan motocin Naira biliyan 3.2 daga 'yan kwangila 10.

Majalisar wakilai take biye da su domin sun siyo motocin Naira biliyan 3 daga ' yan kwangila 17. Hukumar majalisar dattawan ta lullube almubazzarancinta ta hanyar fito da motocin Naira miliyan 430,daga 'yan kwangila biyar.

'Yan kwangilar da suka samarda motocin sun hada da: Lanre Shittu motors(N900miliyan), Mushin Motors (N152miliyan),Sunstar integrated services Limited (N136.4miliyan),Assamad procurement and services limited (N401.2miliyan),Kaffe international investment limited (N115.4miliyan) da stable technology limited (N123miliyan).

Bayan an manna musu kudin da zasu kashe a shekarar 2018 har naira biliyan 125, hakan bai ishe su ba, banda uban albashi da suke diba daga lalitar gwamnati, sai kuma gashi wai sun amshi wata Naira biliyan goma daga m'aikatar kudi, ko rabin 2018 din ba'a kai ba.

DUBA WANNAN: Zawarcin kabilar Igbo a 2019

Wannan ba shine lokacin farkon da majalisar dattawan a karkashin shugabancin Bukola Saraki take almubazzarancin siyan kasaitattun motocin ba.

A watan Disamba na 2015,an bankado shirye shiryen majalisar na siyo motocin kimanin Naira biliyan 4.7 duk da halin da kasar take ciki. Rahotannin da aka yada bai dakatar dasu siyan motocin ba.

A watan Augusta 2017,majalisar wakilai tace zata siya motoci kirar Peugeot 508 na kimanin Naira biliyan 6.1 don ma'aikatan ta guda 360.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel