'Yan sanda sunyi caraf da wasu makiyaya dauke da miyagun makamai da kayan sojoji

'Yan sanda sunyi caraf da wasu makiyaya dauke da miyagun makamai da kayan sojoji

A ranar Asabar ne Jami'an hukumar Yan sanda Najeriya suka kama wasu bindogogi da alburusai a yayin da suka tare wata babban mota kirar Toyota Hummer a kan babbar titin Abakalili-Ogoja.

Abin ya afkune da misalin 6:30 na yamma kafin akai gadar nan ta Onu-Ebonyo Nwaezeyi a karamar hukumar Izzi dake Jihar Ebonyi. Wannan abin ya faru bayan wata daya dakai hari inda aka kashe mutane uku a Onunwakpu kusa da inda aka kama su.

'Yan sanda sunyi caraf da wasu makiyaya dauke da miyagun makamai da kayan sojoji

'Yan sanda sunyi caraf da wasu makiyaya dauke da miyagun makamai da kayan sojoji

Motar na dauke da suna "Taraba express" inda yan sandan suka tsaidata domin bincike kafin hawa gadar. Wani ganau daya nemi a boye sunan sa ya bayyana cewa Motar tana dauke da lambar Jahar legos abin ya faru ne da misalin 6:30 na yamma kafin akai gadar Onu Ebonyi.

DUBA WANNAN: Jam'iyyu 42 sun hada kai don mara wa dan takaran shugaban kasa daya baya da zai kallubalanci APC

Akwai Yan sanda a wajen wadanda suke tsayar da ababen hawa sun gano bindogogi a yayin da suka tsayar da Motar domin bincike kamar yanda suka saba.

Sannan sun sami makamai wadanda yawansu yakai 16. Mai maganar ya kara da cewa wadanda ake zargin sun boye makaman ne a cikin buhu yayin da saura n aka sakasu a cikin kwalaye.

A halin yanzu hukumar yan sanda ta Ebonyi ta halarci inda aka kama wannan motar sannan ta bayar da izinin dauke ta daga gurin.

An dauke motar daga gurin bayan umarni da suka samu daga me magana da yawun hukumar yan sandan kasa ASP Loveth Odah. A halin yanzu Motar tana karkashin kulawar headquarter ta police din abakaliki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel