Jam'iyyu 42 sun hada kai don mara wa dan takaran shugaban kasa daya baya da zai kallubalanci APC

Jam'iyyu 42 sun hada kai don mara wa dan takaran shugaban kasa daya baya da zai kallubalanci APC

- A kalla jam'iyoyin siyasa 42 ne suka dau alwashin hada karfi da karfe don goyon bayan dan takara daya da zai kalubalance jam'iyyar APC

- Shugaban taron dangin, Breakforth Onwunbuya yace akwai bukatar su hada kai waje guda don fatali da gwamnatin APC

- Sai dai yace, jam'iyoyin baza suyi maja ba kawai dai zasu goyi bayan dan takara daya ne a zaben shugabancin kasar

Wasu jam'iyyun siyasa 42 sun hada kai waje guda sun kuma amince su fitar da dan takarar shugabancin kasa guda daya wanda zasu marawa baya a zaben shekarar 2019 mai zuwa.

Jaridar Daily trust ta ruwaito cewa sun amince da cewa akwai bukatar yin hakan ne saboda su hada karfi da karfe wajen kawar da jami'iyyar All Progressives Congress (APC) kuma a kafa sabuwar gwamnati a 2019.

Legit.ng ta gano cewa a jawabin da yayi a ranar Juma'a 20 ga watan Afrilu a Abuja, shugaban tafiyar a karkashin kwamitin Concerned Political Parties (CCPP), Breakforth Onwunbuya, yace jam'iyoyin ba zasuyi maja ba amma zasu hade waje guda don marawa dan takara daya baya.

A wata rohoton kuma, Legit.ng ta ruwaito muku yadda wasu 'yan Najeriya suka nuna kin amincewarsu da sake fitowa takarar zabe da shiugaba Muhammadu Buhari ya ambata zaiyi, su kuma magoya bayan shugaba Muhammadu Buhari suna ta kara mara masa baya a tazarcen da ya ke niyyar yi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel