Gwamna El-Rufai ya samu jika ta farko, ya nemi jama'a su taya shi murna

Gwamna El-Rufai ya samu jika ta farko, ya nemi jama'a su taya shi murna

A jiya Juma'a 20 ga watan Afrilu ne, surukarsa gwaman jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai, Kamilah, wanda ke auren dan sa Bello El-Rufai ta haifi diya mace.

Legit.ng ta gano cewa Bello El-Rufai ya bayar da sanarwan ne a jiya ta kafar sada zumunta na Facebook inda ya ce matarsa, Kamilah, ta haifi diya mace kuma ya kara da cewa mahaifiyar da diyar data haifa duk suna cikin koshin lafiya.

Gwamnan jihar Kaduna, El-Rufai ya samu jika

Gwamnan jihar Kaduna, El-Rufai ya samu jika

KU KARANTA: Kalubalen tsaro guda 5 dake cinma shugaba Buhari tuwa a kwarya

Kalamansa: "Dukkan godiya ta tabbata ga Allah. A daren yau misalin 9.36 matata, Kamilah El-Rufai ta haifi diya mace. Dukkansu suna cikin koshin lafiya. Muna rokon addu'a daga gareku. Tabbas, babu ranar farin ciki daya dara wannan a rayuta."

A wata labarin, Legit.ng ta ruwaito muku cewa a ranar, Juma'a 1 ga watan December, gwamna Nasir El-Rufai ya yanke shawarar daukan dawainiyar yara uku da marigayi kwamishinan Ilimi, Kimiyya da Fasaha na jihar, Farfesa Abdrew Nok.

A yayin da yake jawabi a wata taron da aka shirya don karama marigayin Farfesa, El-Rufai yace gwamnatin tarayya zata dauki dawainiyar karatun yara uku da marigayin kwamishinan ya bari har zuwa matsayin karatun digiri na uku wato Phd.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel