Kalubalen tsaro guda 5 dake cinma shugaba Buhari tuwa a kwarya

Kalubalen tsaro guda 5 dake cinma shugaba Buhari tuwa a kwarya

A ziyarar da shugaba Muhammadu Buhari ya kai kasar Ingila, ya shaida wa Prime Ministan, Theresa May cewa yafi mayar da hankali kan batun samar da tsaro da kuma habbaka tattalin arzikin Najeriya sama da neman zarcewa kan mulki.

Sai dai duk da hakan, akan samu labarun kai hare-hare a wasu sassan kasar sau da yawa kuma hakan ne sanya wasu jinjina zancen na shugaban kasar kan yadda yace yafi mayar da hankali kan tsaro. Hakan yasa wasu ke shawartan al'umma su kare kansu don gwamnati ta gaza.

A wannan lokaci da ake kusantar babban zaben 2019, akwai wasu matsalolin tsaro da shugaban kasar ya kamata ya magance kafin shekarar nan ta kare.

1) Boko Haram:

Duk da cewa an samu nasarori sosai cikin yaki da Boko Haram, amma har yanzu yan ta'adan sukan kai hari a wasu wuraren. A wata sabon bidiyo da shugaban kungiyar, Abubakar Shekau ya fitar a ranar 2 ga watan Janairu, ya musanta cewa an ci galaba a kan kungiyar.

An kuma kai hari a garajin Muna inda aka kashe mutane 25 kuma akwai wasu kananan hare-haren da aka cigaba da kaiwa. Bayan hakan kungiyar ta bawa gwamnati kunya bayan da ta sace yan mata 110 a makarantar sakandire na Dapchi a jihar Yobe a ranar 19 ga watan Fabrairu duk da cewa an ceto 104 daga cikin yan matan.

Hakazalika, an samu koma baya cikin sulhun da gwamnati keyi wajan ceto yan matan Chibok inda gwamnatin tace hakan ya faru ne saboda rashin jituwa tsakanin kwamandojin yan ta'adan.

DUBA WANNAN: Kotu ta garkame wani matashi da ya yi kokarin kashe kan sa

2) Rikicin Makiyaya da Manoma

Rikici tsakanin makiyaya da manoma yana ta kara ruruwa tun bayan kashe mutane 73 a akayi a kananan hukumomin Guma da Logo a jihar Benuwe a ranar 1 ga watan Janirun 2018. An cigaba da wasu kashe-kashen musamman a jihohin Taraba, Benuwe da Nasarawa musamman tun bayan kafa dokar hana kiwo da gwamnatin jihar Benuwe ta kafa inda kungiyar makiyaya na Miyetti Allah suka ce basu amince dashi ba kuma zasu tafi kotu.

Duk da cewa gwamnati ta kaddamar da atisayen soji mai taken "Ayem Akpatuma" cikin kwanakin nan an kashe mutane 14 bayan barkewar rikicin a kauyukan Keana, Obi da Awe a jihar Nasarawa.

3) Garkuwa da mutane

Matsalar garkuwa da mutane shima ya sake kunno kai bayan mutane sun fara tsamanin abin ya wuce, a cikin yan kwanakin nan an sace yaran sarkin Ibadan, Oba Lekan Balogun inda suka bukaci kundin fansa naira miliyan 100 kafin daga baya suka rage zuwa miliyan 10 kafin aka sako yaran.

A jihar Kano ma an sace wani Injiya dan kasar Jamus, Michael Cramza mai aiki da kamfanin gine-gine na Dantata, bayan nan an kashe wani dan asalin kasar Syria kuma aka sace dan shi mai shekaru 14 duk a Kano duk da cewa daga bayan an ceto yaron.

A jihar Kaduna kuma an sace shugaban kungiyar direbobin kasa (NURTW), Malam Audu Kano da wasu mukarabansa 6. Ana kara samun rahotanin satar mutanen daga jihohin Kebbi, Legas, Katsina da sauransu.

4) Fashi da Makami

Harin da yan fashi suka kai a Bankuna 5 a garin Offa na jihar Kwara inda mutane 20 suka rasa rayyukansu abu ne wanda zai dade ba'a manta dashi ba duk da cewa Yan sanda sun bayar da sanarwan kama wasu mutane 20 da ake zargi da hannu cikin harin.

Kafin hakan yan bindiga sun kai hari a Kuru-Kuru da Jarkuka a karamar hukumar Anka na jihar Zamfara ind suka kashe mutane, makonni biyu kafin hakan wasu yan bindigan sun kashe mutane 30 a garin Bawar Daji duk a Zamfara.

5) Rikici tsakanin gwamnati da 'yan Shi'a

Ko da shugaban kasar yake Landan inda yake ganawa da Prime Minista, Theresa May, dandazon yan Shi'a sun mamaye Unity Fountain a Abuja inda suke bukatar gwamnati ta saki shugaban su Sheikh Ibrahim El-Zakzaky wanda aka kama tun watan Disambar 2015.

Daga baya yan sanda sunyi kokarin tarwatsa yan Shi'a inda lamarin ya hargitse kuma aka kama yan Shi'a 115. Kakakin rundunar Yan sanda, DSP Anjuguri Manzah, yace yan sanda 22 sun sami raunuka sakamakon hargistin tsakaninsu da yan Shi'a.

Mai magana da yawun kungiyar Shi'a, Ibrahim Musa, ya bayyana cewa yan sandan ne suka bude musu wata yayin da suke tattakinsu na lumana kuma direktan Amnesty International, Dr. Osai Ojigho ya tabbatar da wannan zancen inda yace yan sandan sunyi ganganci.

Da lamau dai yan Shi'an ba za su dena gudanar da irin wannan tattaki ba har sai gwamnatin ta sakon shugaban nasu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel