Dakarun Soji sun dakile wani harin 'yan Boko Haram a jihar Borno

Dakarun Soji sun dakile wani harin 'yan Boko Haram a jihar Borno

Dakarun Bataliyar Sojin kasa mai lamba ta uku na reshen dake gudanar da atisaye da motsa jiki mai taken Lafiya Dole, sun samu nasarar dakile wani harin 'yan ta'adda na Boko Haram a garin Ngamboru Ngala dake jihar Borno.

Kakakin hukumar Texas Chukwu, shine ya bayyana hakan a shafin sadarwa na hukumar Sojin inda ya bayyana cewa, hukumar ta yi nasarar salwantar da rayuwar dan ta'adda guda daya a yayin artabun inda sauran suka tsere sakamakon budar wuta ta dakarun sojin.

Rahotanni sun bayyana cewa, ko shakka ba bu an yi rashin sa'a domin kuwa hukumar Sojin ta rasa wani sojin ta guda daya a yayin musayar wuta da 'yan ta'addan.

Dakarun Soji sun dakile wani harin 'yan Boko Haram a jihar Borno

Dakarun Soji sun dakile wani harin 'yan Boko Haram a jihar Borno

Birgediya Janar Texas ya kuma bayyana cewa, dakarun sojin sun yi nasarar cafke wasu muggan makamai na kare dangi daban-daban da 'yan ta'addan suka tsere suka bari.

KARANTA KUMA: 'Dan Najeriya 1 na mutuwa cikin kowane minti 2 - Likitar Kwakwalwa

Har ila yau hukumar sojin tana ci gaba da tunatar da al'umma akan bayar da hadin kai ga dakarun ta wajen samar da ingatattun rahotanni da za su kawo taimaka wajen dakile duk wani nau'i na ta'addanci.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel