Da dumi-dumi: Kwamandojin Boko Haram da likitansu sun mika wuya

Da dumi-dumi: Kwamandojin Boko Haram da likitansu sun mika wuya

Tiyata kwamandan rundunar Operation Lafiya Dole, Manjo Janar Rogers Nicholas ya bayyana cewa manyan kwamandojin Boko Haram 2 da likitansu sun mika wuya ga hukumar sojin Najeriya.

Ya bayyana hakan ne yayinda ya nunawa jama’a yan Boko Haram din a Maiduguri.

Nicholas ya kara da cewa wata shugabar matan kungiyar tare da yara 3 sun sun mika wuya a Kumshe, karamar hukumar Bama na jihar Borno.

Yace yan ta’addan sun mika wuya da kansu yayinda suka lura cewa za’a karbesu da karamci da mutunci karkashin shirin ‘Safe Corridor Scheme’ da gwamnatin tarayya ta kafa don kira gay an ta’addan sun ajiye makamansu.

Da dumi-dumi: Kwamandojin Boko Haram da likitansu sun mika wuya

Da dumi-dumi: Kwamandojin Boko Haram da likitansu sun mika wuya

Kwamandan ya bayyana cewa sun tuntubi yan Boko Haram din ne inda suka jawo hankulansu da mika wuya. Ya ce da yawa daga cikinsu sun bayyana niyyar yin haka.

Yace: “Mun basu kaya, abinici da kuma magani. Mun tabbatar musu da cewan ba za mu kashe kowa ba.”

KU KARANTA: Jerin sunayen wadanda aka kashe a fashin bankin Offa

Likitansu ya bayyana irin ayyukan da yake musu na cire harsashi daga jikinsu idan suka ji rauni, taimakawa matansu wajen haihuwa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel