Gwamnati ta tarwatsa wasu Gidajen sayar da Barasa da na Karuwai a jihar Jigawa

Gwamnati ta tarwatsa wasu Gidajen sayar da Barasa da na Karuwai a jihar Jigawa

A sakamakon korafe-korafen al'umma na yankin karamar hukumar Hadejia ta jihar Jigawa dangane da yadda wasu 'yan tsirarun mutane ke tafka fasadi a doron kasa na sayar da barasa da kuma harkar karuwanci, rahotanni sun bayyana cewa hukumar tsaro ta jihar ta dauki wasu kwararan matakai.

Majiyar rahoton dai ta bayyana cewa, hukumomin tsaro sun tarwatsa kwalabe na barasa tare da gidajen mashaya da ake sayar da su, yayin da kuma ta kori masu sana'ar karuwanci da rufe gidajen da suke aikata alfasha.

Sashen kwalaben barasa da aka tarwatsa a wata Mashaya

Sashen kwalaben barasa da aka tarwatsa a wata Mashaya

Gwamnati ta tarwatsa wasu Gidajen sayar da Barasa da na Karuwai a jihar Jigawa

Gwamnati ta tarwatsa wasu Gidajen sayar da Barasa da na Karuwai a jihar Jigawa

'Yan Hisbah yayin aiki a wata Mashaya

'Yan Hisbah yayin aiki a wata Mashaya

Rahotanni sun bayyana cewa, wannan cin kashi na fasadi yafi ta'azzara a unguwar Mai Randa dake daura da hanyar jihar Kano a garin Hadejia.

Legit.ng ta fahimci cewa, an gudanar da wannan aikin Allah ne a ranar Alhamis din da ta gabata yayin da hukumomin tsaro dake da hannu cikin wannan abin son barka suka hadar da; hukomomin soji, civil defence, Immigration, Prison Service, Bijilanti, 'yan sanda, DSS, Hisbah da sauransu.

KARANTA KUMA: Maryam Sanda ta nemi mijin ta ya sake ta kafin mutuwar sa - Inji Mashaidi

Sauran masu hannu cikin wannan jihadi sun hadar da, kungiyar Kansilolin kananan hukumomi inda kakakin ta Honarabul Dawaki Baffa ya jagoranci yin tattaki har zuwa mashayar da kuma gidajen na Karuwai.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel