Buhari ka hakura da mulki ko kuma ka fuskanci irin na Jonathan – Babban limami

Buhari ka hakura da mulki ko kuma ka fuskanci irin na Jonathan – Babban limami

- Shugaban cocin Inri Evangelica, Primate Babatunde Ayodele ya bukaci shugaba Buhari da ya sauka daga kujerar shugaban kasa idan kuma ya kiya, ya fuskanci cin mutunci kamar wada ya karba kujerar daga hannunsa

- Ayodele ya bayyana hakane lokacin bikin bude sabuwar cocinsa mai daukar mutane 50,000, inda ya bukaci shugaban majalissar dattijai Bukola Saraki da ya tsaya takarar shugaban kasa a zaben 2019

- Ayodele ya bayyan cewa Ubangiji ya sanar dashi cewa Saraki zai zama shugaban kasa na gaba a Najeriya

Shugaban cocin Inri Evangelica, Primate Babatunde Ayodele ya bukaci shugaba Buhari da ya sauka daga kujerar shugaban kasa idan kuma ya kiya, ya fuskanci cin mutunci kamar wada ya karba kujerar daga hannunsa.

Ayodele ya bayyana hakane lokacin bikin bude sabuwar cocinsa mai daukar mutane 50,000, inda ya bukaci shugaban majalissar dattijai Bukola Saraki da ya tsaya takarar shugaban kasa a zaben 2019.

Ayodele ya bayyan cewa Ubangiji ya sanar dashi cewa Saraki zai zama shugaban kasa na gaba a Najeriya, saboda zai juya ragamar Najeriya zuwa ga cigaba idan har yayi shawarar tsaywa takarar, domin shi takararsa umurni ne daga ubangiji.

Buhari ka hakura da mulki ko kuma ka fuskanci irin na Jonathan – Babban limami

Buhari ka hakura da mulki ko kuma ka fuskanci irin na Jonathan – Babban limami

"A shekarar 2013 mun fadawa Jonathan bazai iya cin zabe ba, kuma muka maimaita masa a shekarar 2014, amma yaki saurarenmu kuma sai gashi ya fadi zabe.

"A zaben shuagaban kasar Laberia na fadawa Georgr Weah cewa sai yayi wasu dabaru sannan zaici zabe.

“Yayi kuma yaci zaben. Sannan mun fadawa Uhuru Kenyatta na kasar Kenya makancin haka kuma shima yayi yaci zabe.

KU KARANTA KUMA: Satar sandar girma ta majalisa rahama ce a lullube - Sanata

"Na fadawa Umara Samara dan takarar shugaban kasa na Sierra Leon, yaki yabi hanyar dana fada masa a cikin sakon dana tura masa da hanyar wakilai na kuma bayan zabe abunda ba’ason dai ya faru”, inji shi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel