Satar sandar girma ta majalisa rahama ce a lullube - Sanata

Satar sandar girma ta majalisa rahama ce a lullube - Sanata

- Sanata Abu Ibrahim (APC- jihar Katsina) ya bayyana harin da ‘yan ta’adda suka kai a majalisa a matsayin wani cigaba

- Yace a ranar Laraba wasu ‘yan ta’adda sun shiga majalisa ana cikin zama a majalisar suka kaiwa wasu mutane hari suka gudu da Sandar Girma

- Sanatan ya faminci cewa harin wata rahama ce a lullube sakamakon lamarin ya bayyana matsalar dake akwai a majalisar game da tsaro

Sanata Abu Ibrahim (APC- jihar Katsina) ya bayyana harin da ‘yan ta’adda suka kai a majalisa a matsayin wani cigaba da majalisar ta samu.

Yace a ranar Laraba wasu ‘yan ta’adda sun shiga majalisa ana cikin zama a majalisar suka kaiwa wasu mutane hari suka gudu da Sandar Girma.

Satar sandar girma ta majalisa rahama ce a lullube - Sanata

Satar sandar girma ta majalisa rahama ce a lullube - Sanata

Sanatan ya faminci cewa harin wata rahama ce a lullube sakamakon lamarin ya bayyana matsalar dake akwai a majalisar game da tsaro, sannan kuma abu na biyu da kara kawowa a majalisar shine hadin kan ‘yan majalissar, lamarin ya kara sanyawa sun sabunta biyayyarsu da rantsuwa game da majalissar da kuma dokar kasa.

KU KARANTA KUMA: Najeriya ta wadata da matasa masu kwazo da kokari - PDP

Sanata Ibrahim yace game kuma da kungiyar masu goyon bayan Buhari ta “Buhari Support Group”, kungiyar zata bude Ofishi a garin Edo, a jihar Akwa Ibom da kuma jihar Cross River, a ranar Litinin, sannan kuma za’a kaddamar da motocin kamfen a ranar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel