Batun cin hancin Diezani da mukarrabanta ya sake taso wa

Batun cin hancin Diezani da mukarrabanta ya sake taso wa

- Kotu tayi barazanar rufe karar su Omokore da akayi na damfarar dala biliyan 1.6

- Mista Omokore abokin tsohon ministan Fetur ne Diezani Allison Madueke

- An tafka sata a mulkin PDP

Batun cin hancin Diezani da mukarrabanta ya sake taso wa

Batun cin hancin Diezani da mukarrabanta ya sake taso wa

Babbar kotun tarayya da ke Abuja, a ranar Alhamis tayi barazanar rufe karar da aka kawo ta Jide Omokore da wasu mutane biyar na zargin su da akeyi na damfarar dala biliyan 1.6 ta Gwamnatin tarayya.

A lokacin da aka kira shari'ar, lauyoyi masu tuhuma, Oluwaleke Atolagbe ya sanar da kotun cewa shugaban su, Rotimi Jacobs (SAN), yana rokon kotun da ta jingine shari'ar.

Mista Atolagbe ya sanar da mai shari'a Nnamdi Dimgba cewa Mista Jacobs ya sanar dashi ranar laraba da dare cewa bai samu shaida ba sakamakon Jarabawar da shaidun, ma'aikatan hukumar yaki da rashawa, da kuma lauyoyin da ke tuhuma suna rubuta Jarabawa.

R. Lawal daya daga cikin lauyoyin masu tuhuma yace"Duk dage sauraron karar da kotun take yi, ba wanda lauyan wanda ake kara ya taba roko

Mai shari'a Dimgba yace ba zai amince da rufe karar ba nan gaba. Amma zai ba masu karar dama daya. Ya dage sauraron karar zuwa 26 da 27 ga watan Afirilu don masu tuhuma su kawo shaidun su.

DUBA WANNAN: Agajin gwamna Geidam ga ma'aikata

Ana tuhumar Mista Omokore tare da Victor Briggs, tsohon shugaban kamfanin cigaban man fetur da Abiye Membere, zababben shugaban kungiyar hako man fetur na matatar mai.

Tare dasu akwai David Mbanefo, tsohon shugaban tsari da kasuwanci na matatar mai, da laifin kwashe dala biliyan 1.6 na ma'aikatar mallakin Gwamnatin tarayya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel