Saraki ya nisantar da kansa da lamarin damfara na N10bn, ya jinginawa masu watsa labarai

Saraki ya nisantar da kansa da lamarin damfara na N10bn, ya jinginawa masu watsa labarai

- Shugaban majalisar Dattijai Dr. Bukola Saraki a ranar Juma’a ya karyata bayanai da aka fitar a kafar watsa labarai ta yanar gizo akan cewa yana da hannu a cikin damfara da akayi ta N10bn

- Mai bawa shugaban majalisar shawara ta fannin labarai da jama’a Yusuph Olaniyonu ya bayyana cewa Saraki bashi da hannu a cikin wata damfara ko rashin gaskiya ko fitar da wasu kudi wadanda basa cikin kasafin majalisar

- Yusuph yace mun samu labarin cewa wasu masu watsa labarai sun bayyana cewa Dr. Abubakar Bukola Saraki yana cikin rikin wasu kudi da suka raba Janar na kudi da kuma minister Adeosun N10bn

Shugaban majalisar Dattijai Dr. Bukola Saraki a ranar Juma’a ya karyata bayanai da aka fitar a kafar watsa labarai ta yanar gizo akan cewa yana da hannu a cikin damfara da akayi ta N10bn.

Mai bawa shugaban majalisar shawara ta fannin labarai da jama’a Yusuph Olaniyonu ya bayyana cewa Saraki bashi da hannu a cikin wata damfara ko rashin gaskiya ko fitar da wasu kudi wadanda basa cikin kasafin majalisar.

Yusuph yace mun samu labarin cewa wasu masu watsa labarai sun bayyana cewa Dr. Abubakar Bukola Saraki yana cikin rikin wasu kudi da suka raba Janar na kudi da kuma minister Adeosun N10bn, ba tare da suna da wata kwakkwarar shaida ba.

Saraki ya nisantar da kansa da lamarin damfara na N10bn, ya jinginawa masu watsa labarai

Saraki ya nisantar da kansa da lamarin damfara na N10bn, ya jinginawa masu watsa labarai

Ya kara da cewa duk da gargadin da akayiwa masu watsa labarai amma bai hanasu kirkira labarin karya ba sun jinginashi da shugaban majalisar.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Wata ‘yar Najeriya ta kara samun babban matsayi a majalisar dinkin duniya

Akwai lauyan Dr. Bukola Saraki yana nan yana kokarin gano wadanda suka fada wannan labara don yayi kararsu a gaban kotu. Sannan muna rokon mutane da kadasu amince da wannan labara koda ya ganshi, koya gani ya daukeshi a matsayinsa na karya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel