Mun gama da Boko Haram: Janar Buratai ya sake nanatawa ga duniya

Mun gama da Boko Haram: Janar Buratai ya sake nanatawa ga duniya

- Buratai ya tabbatar da cewa an fi karfin Boko Haram, an shirya hada kan 'yan gudun hijira

- Duk da' yan kunar bakin wake a Arewa maso gabas, sojojin Najeriya a ranar Alhamis sun ce a fatattaki kungiyar Boko Haram

- "Daukacin rundunar sojojin zasu koma Borno don dawo da wadanda suka bar ta sannan zamu zauna dasu na wata hudu ko biyar"

Mun gama da Boko Haram: Janar Buratai ya sake nanatawa ga duniya

Mun gama da Boko Haram: Janar Buratai ya sake nanatawa ga duniya

Shugaban sojojin Lieutenant General Tukur Buratai, ya fadi haka a tataunawar waya da yayi da manema labarai. Wanda, taron United States Mission, Nigeria to wrap up the African Land Forces, 2018 ta shirya da hadin guiwar kwamandan US Army Africa, Gen. Eugene LeBoeuf.

Yace ana shirye shiryen maida 'yan gudun hijirar zuwa garuruwansu a Borno. 'Yan gudun hijirar da suka tsere suka bar guraren zaman su sakamakon hare haren 'yan Boko Haram, za a maida su gidajen su tare da tsaron sojoji na wata hudu ko biyar "

A lokacin da wani manemin labarai ya tambayeshi cewa duk da sojojin suna kara tabbatar da cewa an fatattaki 'yan ta'addan amma bashi yasa aka daina Jin tashin hankalin da suke haddasawa ba.

Yace "Da farko dai ka duba daga inda muke, ina muke da kuma ina zamu je. A da Boko Haram suna walwalar su a duk inda suke so a fadin kasar nan. Kafin 2015, sun kai Abuja, Lokoja, Sokoto, Kano, Kaduna, Jos, Bauchi".

Kai a takaice ma duk sassan kasar nan ballantana arewa da wasu sassan tsakiyar kasar. Amma tun 2016 babu harin da aka kaiwa wajen arewa maso gabas. A 2017, babu wani babban hari da aka kai Arewa maso gabas. A wannan lokacin kuwa nasan zaku yarda cewa mun fi karfin Boko.

"In dai a Maiduguri kake ko wani sassan na arewa maso gabas, zaka yarda cewa Boko Haram ta mutu. A shekaru biyu da suka wuce bama dajin sambisa amma yanzu muna cikin shi"

"A iya sanina, nasan mun fatattaki Boko Haram, mun wuce nan. Wasu ma daga cikin 'yan gudun hijira sun fara komawa garuruwansu."

DUBA WANNAN: An kara wa Magu girma

"Dole ne muyi amfani da duk karfin mu don samar da abubuwan more rayuwa kamar makarantu, asibitoci domin su dawo garuruwansu."

"Dukkan rundunar sojojin zasu koma Borno don dawo da wadanda suka bar ta sannan zamu zauna dasu na wata hudu ko biyar."

Buratai yace akwai bukatar kasashen Afirika su hada kai don yaki da ta'addanci.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel