Gwamnatin tarayya ta damu da cigaban matasa - Ministan Buhari

Gwamnatin tarayya ta damu da cigaban matasa - Ministan Buhari

- Ministan labarai da al’adu Alhaji Lai Mohammed ya bayyana cewa gwamnatin tarayya a karkashin shugaba Muhammadu Buhari ta damu damu da cigaban matasa

- Mohammed ya karayata maganganu akan cewa shugaba Buhari ya nuna cewa matasan Najeriya ‘yan cima zaune ne wadanda basu son yin aiki

- Mohammed yace yana mamakin yanda wasu basu da aikin yi banda su zauna suna juya maganganun da shugaba Buhari yayi suna basu wata mummunar fasara

Ministan labarai da al’adu Alhaji Lai Mohammed ya bayyana cewa gwamnatin tarayya a karkashin shugaba Muhammadu Buhari ta damu damu da cigaban matasa, ya bayyana hakane a ranar Juma’a 20 ga watan Afirilu 2018.

Mohammed ya karayata maganganu akan cewa shugaba Buhari ya nuna cewa matasan Najeriya ‘yan cima zaune ne wadanda basu son yin aiki, ministan yayi wannan jawabi ne a garin Abeokuta lokacin da yake zantawa da manema labarai a wurin bikin al’adu na Afirika.

Gwamnatin tarayya ta damu da cigaban matasa - Ministan Buhari

Gwamnatin tarayya ta damu da cigaban matasa - Ministan Buhari

Mohammed yace yana mamakin yanda wasu basu da aikin yi banda su zauna suna juya maganganun da shugaba Buhari yayi suna basu wata mummunar fasar, yace yana mamakin yanda za’ace gwamnatin data samawa matasa 100,000 aikinyi kuma take ciyar da yara miliyan 7.5 a kowace rana, ace itace ke sukar matasan kuma.

KU KARANTA KUMA: Najeriya ta wadata da matasa masu kwazo da kokari - PDP

Bikin al’adun wanda aka fara a ranar Alhamis da jihohi 20 da kuma kasashe 40, tare da al’adu kusan 30 iri daban daban wadanda suka halarci bikin zai kare ne a ranar Asabar 21 ga watan Afirilu na shekarar 2018.

A halin da ake ciki, Sakataren jam’iyyar ta PDP ya bayyana cewa kalaman da shugaba Buhari yayi game da matasan Najeriya ya raunata masu tinaninsu ga idon duniya data sansu da kwazo.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel