Lafiya dole: Wasu mayakan kungiyar Boko Haram sun saduda, sun mika wuya ga sojojin Najeriya

Lafiya dole: Wasu mayakan kungiyar Boko Haram sun saduda, sun mika wuya ga sojojin Najeriya

- Wasu 'yan kungiyar Boko Haram sun guda bakwai mika wuya ga sojojin Najeriya a jihar Borno

- Daga cikinsu har da likita guda daya wanda ya ke cire harsashi daga jikin mayakan Boko Haram

- 'Yan Boko Haram din sun ce wahala ta ta ishe su har yasa suka fito daga daji suka mika wuya

Dakarun sojojin Najeriya ta Operation Dole ta bayyana cewa wasu mayakan kungiyar Boko Haram sun mika wuya a karamar hukumar Bama da ke jihar Borno. Mutanen da suka hada kansu sun hada da maza guda biyu da mace guda daya da kuma kananan yara guda biyu.

Lafiya dole: Wasu mayakan kungiyar Boko Haram sun saduda, sun mika wuya ga sojojin Najeriya

Lafiya dole: Wasu mayakan kungiyar Boko Haram sun saduda, sun mika wuya ga sojojin Najeriya

Kamar yadda muryar Amurka ta ruwaito, cikin mutane bakwai da hukumar soja ta gabatarwa manema labarai akwai maza guda biyu da ta ce manyan yan Boko Haram ne da suka mika wuya da kansu a wani gari mai suna Kumshe da ke karamar hukumar Bama a jihar Borno.

DUBA WANNAN: An saka ladan N500,000 a kan 'yan bindiga da suka kashe dan sanda a caji ofis

A yayin da yake yiwa manema labarai bayani, Kwamandan dake kula da Operation Lafia Dole a Arewa maso gabashin Najeriya, Manjo Rogers Nicholas, yace mutanen sun kira sun ce sun tuba kuma akwai karin wasu mutane da yawa a cikin daji da ke son mika wuya.

Sun kuma ce, sun fara fitowa su mika kansu ne saboda su tabbatar da cewa ba za'a kashe su ba, daga bisani kuma su koma su fadawa yan uwansu da ke daji su fito suma su mika wuya.

Daya daga cikin yan Boko Haram din daya ce sunansa Husaini Ali Dakta, ya ce shine likitan dake yin tiyatar cire harsashi a jikin mutane kuma yana taimakawa mata yayin haihuwa a sansanin mayakan Boko Haram din.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel