Kotu ta garkame wani matashi da ya yi kokarin kashe kan sa

Kotu ta garkame wani matashi da ya yi kokarin kashe kan sa

- Kotu ta tsare wani matashi, Andrew Peter, saboda yayi yunkurin kashe kansa

- Yan sanda sun kama Peter ne bayan ya saci wayan salula a kuma yayi kokarin guduwa amma daga baya aka sake kamo shi

- Alkalin kotu ya bayar da umurcin a tsare shi saboda girman laifin daya aikata

A yau Juma'a ne wata kotun Majistare dake zama a Osogbo ta bayar da umurnin tsare wani matashi mai shekaru 23, Andrew Peter, a kurkukun garin Ilesa saboda yayi yunkurin kashe kansu yayin da yake tsare a ofishin Yan sanda.

Kotu ta garkame wani matashi da ya yi kokarin kashe kan sa

Kotu ta garkame wani matashi da ya yi kokarin kashe kan sa

Alkalin kotun, Mr. Olusegun Ayilara, ya ce a tsare matashin saboda girman laifin daya aikata.

KU KARANTA: Lafiya dole: Wasu mayakan kungiyar Boko Haram sun saduda, sun mika wuya ga sojojin Najeriya

Dan sanda mai shigar da kara, Sufeta Lamidi Rasaki ya shaida wa kotu cewa wanda aka gurfanar ya saci wayar salula ne a watan Afrilu a unguwar Okefia a garin Osogbo kuma aka tsare shi a caji ofis.

Ya kuma ce an kai Peter asibiti don yi masa magani amma daga baya ya sake tserewa amma daga baya aka sake kamo shi.

Wanda ake tuhumar ya amsa laifi guda uku da ake tuhumarsa dashi wanda suka sabawa sashi 327, 192 da 135(9) na dokar criminal code cap 34 vol. 11 na jihar Osun, 2003.

Duka da haka, alkalin kotun ya dage sauraron karar zuwa 27 ga watan Afrilu don a kara gabatar da bayyanai a kan shari'ar kafin ya yanke hukunci.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel