Fata na ku bar dana ya gaje ni - Sarauniya Ezzabil ga shuwagabannin kasashen Commonwealth

Fata na ku bar dana ya gaje ni - Sarauniya Ezzabil ga shuwagabannin kasashen Commonwealth

- Anyi taron kasashen CommonWealth an gama

- Kasashen da Ingila ta girma sune Common Wealth

- Kasashen su 53 ne

Fata na ku bar dana ya gaje ni - Sarauniya Ezzabil ga shuwagabannin kasashen Commonwealth

Fata na ku bar dana ya gaje ni - Sarauniya Ezzabil ga shuwagabannin kasashen Commonwealth

Ku bar 'da na ya gaje ni, sarauniya Elizabeth ta roki shuwagabannin gwamnatocin Commonwealth a taron da aka fara ranar Alhamis a Buckingham Palace a tsakiyar birnin Landan.

Duk da sarauniya Elizabeth ta gaji mahaifinta, Sarki George na 6,wanda ya mutu sakamakon sankarar huhu a 1952,matsayin sarauniya ko sarkin ingila na shugaban Commonwealth ba gado bane.

Shugaban ta roki shuwagabannin dasu bar Yarima Charles ya maye kujerarta, ta shugaban Commonwealth bayan shudewar zamanin ta.

Kamar yanda mahaifinta ya fadi a wannan gurin a 1949, kasashe 8 ne kacal a kungiyar. Amma yanzu sun kai 53 da kuma mutane biliyan 2.8.

Sarauniyar ta roka ne domin daidaituwa da cigaba, 'dan ta wanda shine Yariman Wales ya cigaba da aiyukan ta, tabbatar da cewa kungiyar zata cigaba da bunkasa da habaka.

"A gaskiya zanso Commonwealth ta daidaita da cigaba har zamani mai zuwa kuma zanso Yariman Wales ya cigaba da muhimman aiyukan da mahaifina ya fara a 1949" tace kafin zagayowar ranar haihuwar ta ta 92 a ranar asabar.

"Idan muka cigaba da tattali da bunkasa kungiyar mu da aiyukan mu, tabbas 'yan baya zasu tarar da cigaban. A lokacin ne karamcin Commonwealth zai warkar kuma ya ba ma kowa buri " tace.

DUBA WANNAN: Martanin PDP ga Buhari

Rahoton BBC yace wannan ne lokaci na farko da Sarauniyar ta taba maganar gadonta a cikin jama' a kamar yanda tace bata da karfin doguwar tafiya don haka bazata samu halarta taro na gaba da za'ayi a Malaysia a 2020 ba.

An ruwaito cewa a taron da za'ayi a Windsor, Landan, za'a tattauna zancen gadon da Sarauniyar ta tado.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel