An kai wa jami’an tsaron Saudiyya mummunan hari, mutane 4 sun mutu

An kai wa jami’an tsaron Saudiyya mummunan hari, mutane 4 sun mutu

- Wasu yan bindiga sun kai mummunan hari kan jami'an tsaron kasar Saudiyya

- Mutane hudu sun mutu sannan wasu hudu sun jikkata

- An damke biyu daga cikin maharan

Rahotanni dake zuwa mana daga kasar Saudiyya ya nuna cewa mutane hudu sun hallaka inda wasu hudun suka ji raunuka sanadiyan mummunan harin da aka kai wa jami’an tsaron kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Kasar ya rawaito kakakin Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida Manjo janar Mansur Al-Turki na cewa, an kai wa jami’ansu hari a wani shingen binciken ababan hawa dake tsakanin jihohin Al-Majaride da Barik a kudo maso-yammacin Kasar.

Ya ce, Ahmed Ibrahim Asiri, Abdullah Gazi Al-Shahri da Salih Ali el-Umari ne suka rasa rayukansu kuma jami’an tsaro sun damke 2 daga cikin wadanda suka kaddamar da harin.

KU KARANTA KUMA: Ka janye maganarka sannan ka ba matasan Najeriya hakuri – Shehu Sani ya shawarci Buhari

Haka zalika wasu mutane hudu sun jikkata sanadiyan fafatawar da akayi.

Hakan na zuwa ne daidai lokacin da yariman kasar Saudiyyan mai jiran gado ke kawo sababbin sauye-sauye a birnin ta yadda suma za'a dama dasu a kasashe masu tafiya da zamani.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel